Connect with us

LABARAI

Don Inganta Tsaron Kasa: Shugaban NIS Ya Bude Sabon Babin Kula Da Shige Da Fice

Published

on

A ci gaba da kokarin da take yi wajen inganta ayyukanta domin sanya Nijeriya ta yi alfahari tare da gogayya da kasashen duniya da suka bunkasa, Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS), ta gabatar da Kundin Matakan Kula da Iyakokin kasa da za a yi aiki da shi a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023.
Kundin wanda shugaban NIS, Muhammad Babandede ya gabatar a bainar masu ruwa da tsaki na sashen shige da fice a Abuja, ya kudiri aniyar inganta tsaron kasa.
Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya ya ruwaito cewa, kungiyar Tarayyar Turai (EU) ce ta dauki nauyin aikin tsara kundin, yayin da ita kuma Hukumar Kula da Shige da Ficen Baki ta Duniya (IOM) ta aiwatar.
Da yake gabatar da jawabi a taron kaddamar da kundin, Babandede ya yi bayanin cewa Kundin baya ga tsaron kasa da zai inganta, har ila yau zai kuma ba da gudunmawa ga bunkasa tattalin arzikin kasa, da tabbatar da walwalar jama’a tare da tabbatar da kare hakkin baki da kuma ba da kariya ga bakin da aka tilasta musu barin kasashensu na asali.
“Kundin Matakan Kula da Iyakon kasan na 2019 zuwa 2023 ya fito da kudirin da ake son cimmawa baro-baro a fili a cikin shekaru biyar masu zuwa da kuma fayyace hanyoyin da hukuma za ta bi wajen kula da iyakokin Nijeriya. Wannan duka a karkashin hurumin da NIS take da shi ne,” in ji Babandede.
Bugu da kari, shugaban na NIS, ya ce matukar tsaron kan-iyakokin kasa ya inganta, kasa za ta kasance cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
“Saboda haka, kundin ya yi tanadin magance matsalar tsaron kasa, da tsaurara tsaron iyakoki da kuma tsara kan-iyakoki su zama hanyoyin hada-hadar kasuwanci da kasa za ta karu da su.
“Kundin zai kuma tabbatar da gudanar da aiki cikin gaskiya da rikon amana, zai rage cin hanci da rashawa, zai taimaka wajen tabbatar da cewa ana kare hakkin dan Adam, sannan za mu yi tsayin-dakar ganin mun hana masu fasa-kwauri da safarar bil’adama cin karensu ba babbaka wajen shiga ko fita cikin kasar nan,” in ji Babandede.

Shugaban NIS Muhammad Babandede MFR (a tsakiya) tare da sauran masu ruwa da tsaki kan sha’anin shige da fice, jim kadan bayan kaddamar da Kundin.

 

A nashi bangaren, shugaban kwamitin kula da al’amuran cikin gida na Majalisar Wakilai ta kasa, Nasir Daura ya bayyana cewa kwamitin zai yi kokarin ganin an bai wa Hukumar NIS duk goyon bayan da ya kamata don tabbatar da aiwatar da tsare-tsaren da aka yi a kundin.
Ya kara da cewa Kundin zai taimaka gaya ta fuskar ba da kariya ga barin take ‘yancin dan Adam da kiyaye mutuncinsa. Yana mai cewar, “a matsayinmu na kwamiti za mu karfafa Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa domin ta kara kwazo ta hanyar ba ta goyon baya a kasafin kudi ta yadda za ta kula da iyakokin kasa da kyau.”
A jawabinta ita ma, Ministar Kudi da Kasafi da Tsare-tsaren kasa, Hajiya Zainab Ahmed, ta ce samun nasarar aiwatar da matakan da kundin ya tsara ya ta’allaka ne ga yin aiki tukuru daga mahukunta ba fada a baki kawai ba, da kuma samun goyon bayan shugabanni.
Hajiya zainab, wacce wani ma’aikaci mai kula da bangaren shige da fice a ma’aikatarta, Mista Ekom Umoren ya wakilta, ta ce za a shawo kan karuwar aikata miyagun laifuka a tsakanin iyakokin kasa, da shige da ficen baki ta haramtacciyar hanya, da safarar bil’adama kamar yadda aka tsara a manufofin bunkasa ci gaban kasa da ke kunshe a cikin shirin Farfado da Tattalin Arziki na Gwamnatin Tarayya.
Wakazalika, Babban Kwamishin a Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Bakin Waje da Mutane Masu Neman Mafaka, Basheer Mohammed ya halarci taron bisa wakilcin Mista Charles Anaelo.
Ya yi bayanin cewa Kundin alama ce a fili ta dukufar da Nijeriya ta yi wajen yin kafada-da-kafada da kasashen duniya da suka ci gaba a fannin kula da iyakokin kasa.
Ya kara da cewa kula da iyakokin kasa kamar yadda ya kamata, yana da matukar tasiri ga daukacin aikin kula da shige da ficen baki.
“Ba mu da shakkar cewa za a hada karfi da karfe wurin aiwatar da tsare-tsaren kundin domin tabbatar da komai ya tafi dai-dai-wa-dai-da,” in ji shi.
Har ila yau, Babbar Jami’ar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Duniya, Misis Ukamaka Osigwe ta yi bayanin cewa ba su yi gaban-kai wajen tsara kundin ba, sai da suka tuntubi Hukumar NIS da sauran hukumomin da abin ya shafa wanda ya daukesu tsawon lokaci daga watan Oktoban bara zuwa na Maris din 2019.
Ta ce babban dalilin da ya sa aka tsara kundin shi ne fito da kwararan hanyoyin da za a inganta kula da shige da ficen baki a Nijeriya a karkashin ayyukan hukumar da ke jagorantar lamarin, wato NIS.
Bakidaya dai za a iya cewa, sabon Kundin na matakan inganta kula da iyakokin kasa; daya ne daga cikin sauye-sauyen da hukumar NIS ke aiwatarwa bisa shugabancin Muhammad Babandede domin tabbatar da tsaron kasa, bunkasa tattalin arziki da yin aiki cikin gaskiya da rikon amana, kamar yadda yake kunshi a cikin kudurorin gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: