Connect with us

LABARAI

Gwamna Zulum Ya Ziyarci ’Yan Gudun Hijirar Borno 60,000 Da Ke Kamaru

Published

on

A kokarin sa na kula da jin dadi da kyautata rayuwar jama’ar Borno, Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai wa ‘yan gudun hijirar Borno wadanda ke zaune a jamhuriyar Kamaru ziyara ta musamman, a ranar Laraba don ganin halin da suke ciki. Yayin da ya gana da yan hijira sama da 60,000 daga bangarorin jihar daban-daban da rikicin Boko Haram ya tilasra musu barin yankunan su.

Gwamana Zulum ya kai ziyarar domin karfafa goyon baya ga yan hijirar tare da kokarin aiwatar shirye-shiryen dawo dawo dasu yankunan su don sake gina garuruwan su da aka samu kwamciyar hankali.

Bugu da kari kuma, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya (UNHCR), wadda kuma ke kula da wannan matsuguni da ke garin Minawao da Gwamnan ya ziyarta, sansanin da a baya ya kunshi ‘yan gudunhijira 86,000, dukan su ‘yan asalin jihar Borno ne, wadanda ke zaune a kasar Kamaru.

Bayanan da Gwamnan ya samu a hukumance, a lokacin ziyarar, tsara shirin dawowar ‘yan gudun hijirar an tsara shi ne bisa ga ra’ayin kan su ne. Garin Minawa mai kimanin tazarar kilo mita 95 daga babban birnin jamhuriyar Kamaru- Marwa, daga yankin arewacin kasar.

Gwamna Zulum ya tashi ne filin jirgin sama na kasa da kasa, da ke birnin Maiduguri zuwa birnin Marwa, da yammacin ranar Talata. Har wala yau kuma, gwamnan yankin arewacin Kamaru, Mijinyawa Bakare ne tare da manyan jami’an gwamnati ne suka tarbi Gwamna Zulum.

A lokacin da yake yi wa dandazon ‘yan gudunhijirar jawabi, Babagana Umara Zulum ya karfafa musu gwiwa tare da bayyana musu kokari da shirin sake farfado da gina gidajen su a yan kwanakin nan a cikin garuruwan Banki, Bama, Pulka, Gwoza da Darajamal, nan da watani biyu masu zuwa don sake tsugunar da su a lokacin da suka dawo gida.

A hannu guda kuma, Gwamna Zulum ya yaba matuka ga gwamnatin jamhuriyar Kamaru tare da jama’ar yankunan da yan hijirar ke zaune a ciki dangane da halin girmamawa da tausayi da suka nuna wa yan Nijeriya wadanda suka fito daga jihar Borno, wadanda suka gudun hijira a kasar tun a 2013 da 2014, ta dalilin kazantar matsalar tsaro wadda ta jawo maharan Boko Haram mamaye kimanin kananan hukumomi 20 a jihar.

Ana sa ran Gwamnan ya ziyarci karin wasu ‘yan gudun hijirar, wadanda ke zaune a garuruwan da ke kan iyakar jihar Borno da Kamaru, wanda a can ma zai gana da dubun-dubatar ‘yan gudunhijirar.

Zulum ya tafi jamhuriyar Kamaru ne tare da rakiyar shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA), yan majalisar dokoki da kwamishinoni guda biyu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: