Connect with us

LABARAI

Har Yanzu Mutum 165, 631 Ba Su Karbi Katin Zabensu Ba A Kogi- INEC

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta bayyana cewa har yanzu akwai katin zabe 165,631 wadanda ba a karba ba a jihar Kogi ya zuwa ranar 13 ga watan Satumba.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin da take karin haske dangane da karbar katin zaben a jihar wanda aka fara a ranar 2 ga watan Satumba, a shirye-shiryen zaben 16 ga watan Nuwamba da zai gudana a jihar.

Rahoton INEC din ya tabbatar da cewa cikin makonni biyu an karbi katin zabe 5,269 a Kogi cikin  170,900.

Sakataren watsa labarai ga shugaban INEC din, Rotimi Oyekanmi ya shawarci wadanda suka yi katin zaben da su hanzarta su je su karbi katinsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: