Connect with us

KASASHEN WAJE

Harin Ta’addanci Ya Hallaka Mutum 39 Da Raunata 140 A Afghanistan

Published

on

Harin kunar bakin wake da kungiyar Taliban ta kai a wani asibiti dake Kudancin kasar Afghanistan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 39 nunki bisa sanarwar farko na mutuwar mutum 20, kamar yadda Kakakin Gwamnan yankin ya tabbatar a ranar Juma’a.

Adadin wadanda suka jikkata a ranar Alhamis a harin Qalat, birnin Zabul ya kai mutum 140 kamar yadda Gul Islam Syaal ya tabbatar. Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya labarto cewa; mutum biyu ne kawai cikin jami’an tsaro suka rasa rayukansu, a yayin da sauran dukka fararen hula ne wanda ya hada mata, kananan yara da kuma maziyarta da marasa lafiya.

“An tarwatsa asitin baki daya.” Kamar yadda ganau ya tabbatar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: