Connect with us

LABARAI

NUP Ta Bukaci Gwamnoni Su Biya Giratuti Da Waiwayar Fansho

Published

on

Kungiyar Masu amfar fansho ta kasa (NUP) ta roki gwamnonin jihohi da su yi kokarin biyan basukan giratuti da a ke bin su, kana su kuma waiwaya da bibiyar fansho duk bayan shekara biyar-biyar.

A gefe guda kuma, kungiyar ta jero wasu daga cikin gwamnonin arewa maso gabas da suka fara tabuka abun a zo a gani wajen biyan basukan giratuti da ke kawukansu ya zuwa yanzu, suna masu kuma kiran wadanda basu motsa ba, da su motsa domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa, shiyyar arewa maso gabas, Alhaji Muhammad Inuwa Ahmad shine yayi wannan rokon a wata kwafin sanarwar manema labaru da ya fitar a Bauchi, yana mai daurawa da cewa, masu amsar fasho da suka sadaukar da karfinsu da lokacinsu wurin yin aiyuka tukuru wa jihohinsu suna tsananin bukatar gwamnatoci su taimaki rayuwarsu.

Sanarwar ta kuma shaida cewar a matsayin masu amsar fansho na dattawa, gwamnatoci daban-daban sun yi alkawuran cewar za su biyasu hakkokinsu idan suka samu zarafin dalewa kan karagar mulki, don haka ne suka ce akwai bukatar a cika wadannan alkawuran domin masu amsar fansho su ma rayuwarsu ta inganta.

A bisa haka ne suka nuna kwarin guiwarsu na cewar gwamnatocin za su yi kokarinsu wajen sauke basukan giratuti da biyan fansho da ke kawukansu, a bisa haka ne suka nemi ake bibiyar kudaden da ake biya na fansho duk bayan shekara biyar domin kyautata tsarin.

A cewar Alhaji Muhammad Inuwa, “Yanzu haka wasu gwamnonin arewacin Nijeriya sun fara hubbasawa wajen biyan kudaden giratuti da fansho, misali a jihar Bauchi, gwamna Bala Muhammad ya biya naira miliyan 100 wa ‘yan fansho a watan Agustan, sannan a watan Satumba kuma ya sake biyan naira miliyan 200 domin rage basukan fansho na kananan hukumomi da jihar, tare da tsammanin sake samun kaso mafi girma duk wata domin biyan wadannan basukan,” A cewarshi.

“Gwamna  Babagana Umar Zulum na jihar Borno shi ma yayi yunkuri mai kyau na biyan naira biliyan daya a watan Yuli da Agustan domin biyan ‘yan fanshon da suke jihar, tabbas da irin wannan kokarin za a iya kyautata harkar fansho sosai,” a cewar Sanarwar.

Mataimakin shugaban, ya kuma kara da cewa, “Haka zancen yake, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya biya naira biliyan daya da miliyan dari wa ‘yan fanshon da suke bin gwamnatin jihar; muna fatan a yi irin wannan biyan ga ‘yan fanshon da suke kananan hukumomi su ma, muna kuma da kwarin guiwar cewar kowace wata za a ke samun kason da ke fita, har ta kai ‘yan fansho suna cike da annashuwa a kowani lokacin, muna godiya,” A fadin sanarwar.

“Wani karin cigaba ma, shi ma Gwamna Mai-Mala Buni na jihar Yobe ya biya Naira miliyan shida domin biyan basukan giratuti,” a bayanin.

A gefe guda da yake jinjina wa gwamnocin da suka rage basukan giratuti da ke kawukansu, Alhaji Muhammad Inuwa Ahmad ya kuma ayyana gwamnonin jihar Adamawa da na Taraba a matsayin wadanda har yanzu basu samu kudaden giratutin da suke bi ba, yana mai fatan gwamnonin za su motsa nan gaba kadan.

A cewarsa akwai gayar bukatar gwamnatoci suke duba halin da masu amsar fansho ke ciki domin kyautata musu rayuwa, a cewarshi dattawa ne wadanda suke neman agaji biyo bayan kammala aiyukan raya jihohinsu da suka yi.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: