Connect with us

MANYAN LABARAI

Sakamakon Taron Tattalin Arzikin Kasa:Za A Kashe Naira Biliyan 100 A Shirin Bunkasa Kiwon Dabbobi, Somin-tabi

Published

on

  • Bukatar Sake Duba Yarjejeniyar ECOWAS Kan Kiwo Ta Sake Kunno Kai

Majalisar Tattalin Arzikin Kasa ta bayyana cewa shirin bunkasa kiwo na zamani ba zai karkata ne kawai ga bunkasa kiwon shanu ba, zai hada da magance abubuwan da suke kawo cikas ga kiwon sauran dabbobi.

Gwamna Dabid Umahi na Jihar Ebonyi ya bayyana haka sa’ilin da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa a jiya, jim kadan bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa bisa jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Ya nanata cewa makasudin shirin shi ne ya kawo karshen rikicin da ake yi a tsakanin makiyaya da manoma.

“Shugaban Majalisar Tattalin Arzikin Kasa ya tuntar da mu cewa babban burin majalisar shi ne lalubo bakin zaren rikicin manoma da makiyaya. Kwamitin majalisar ya gabatar da tsarin da za a bi a shawo kan lamarin da za a yi aiki da shi daga 2019 zuwa 2028 a yau (jiya), ba kiwon shanu kawai za a bunkasa ba, har da sauran dabbobi na gida da ake kiwo.”

Umahi ya ce tsarin ya kunshi muhimman ayyuka guda shida da suka hada da warware sabani, yin adalci ga kowa da tabbatar da zaman lafiya, ba da agaji ga al’umma, samar da kwararan ma’aikata da sauran batutuwa da suka kunshi bunkasa tattalin arziki.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: