Connect with us

LABARAI

Tsaffin ’Yan Bindiga Sun Bai Wa Kamfanonin Hakar Mai Wa’adin Kwanaki 14

Published

on

Kungiyar ‘yan tsagera ta Neja Delta, wacce ta kunshi tsaffin ‘yan bindiga ta baiwa hukumar hako man fetur ta, Universal Energy Limited a Jihar ta Akwa Ibom, wa’adin kwanaki 14 da ta biya masu bukatunsu guda biyar ko kuma su fuskanci hare-hare a kan kayayyakin su.

Cikin wata sanarwa da ta fito a bayan taron da gamayyar kungiyoyin na Niger Delta Militants, suka yi, wacce kuma ke dauke da sa hannun Ekpo Ekpo da Okon Edemekong a madadin sauran a Uyo, babbar birnin Jihar a jiya, kungiyar ta yi barazanar kai hari da kuma lalata duk wasu cibiyoyin mai da manyan famfunan da ke kai man da kamfanin  ke amfani da su matukar aka kasa biyan masu bukatun na su a cikin kwanaki Bakwai da suka iyakance.

Bukatun na su da suke zargin an cimma yarjejeniya a kansu sun hada da, bayar da kyautar guraben karatu akalla 500 na ilimin gaba da Sakandare, da kuma gurabe 60 ga masu karatun digiri a manyan jami’o’in kasar nan ga ‘yan asalin yankin na Jihar ta Akwa Ibom, samar da mahimman ayyukan raya kasa da kuma samar da wani shiri na musamman na bayar da rancen kudade ga masu kananan sana’o’i, sannan kuma akalla kashi 60 na ma’aikatan da kamfanin zai yi aiki da su su kasance sun fito ne daga ‘yan asalin Jihar.

Sauran sun hada da, daukan ‘yan asalin kauyan Unyenge, a matsayin manyan daraktoci a kamfanin sannan kuma akalla kashi 60 na ayyukan kwangilolin da kamfanin zai bayar ya kasance ‘yan kwangilar sun fito ne daga ‘yan asalin yankin, suna kuma bukatar a samar masu da cibiyoyin kula da lafiyarsu cikin hanzari a yankin na su.

“Matukar aka gaza aiwatar mana da wadannan bukatun na mu a cikin kwanaki 14, ba mu da wani zabi face mu fara kai hare-hare a dukkanin cibiyoyi da tashoshin kamfanin da nufin lalata su, gami da babban bututun mai mai tsawon kilomita 23 da ya taso daga cibiyar Ibeno da kuma sauran kayayyakin kamfanin da ofisoshinsa. A shirye muke da mu sanya ido sosai a kan hakan, ba za mu iya tabbatar da zaman kayayyakin kamfanin gami da ma iyalansu a cikin aminci ba,” in ji sanarwar.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta kama kamfanin da laifi matukar suka yi mata kafar Ungulu a wajen barin kyakkyawan dangantakarta da al’ummun ta lalace wacce aka kulla ta a shekarar 2009.

Duk kokarin da wakilinmu ya yi na yin Magana da babban daraktan Kamfanin, Mista Bassey Umoh, kan bukatun mutanen ya ci tura, domin layukan wayarsa ba sa tafiya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: