Connect with us

BABBAN BANGO

Yadda Gyatuma Mai Shekaru 82 Ta Koma Sararin Samaniya

Published

on

 Miao Xiaohong na daya daga cikin rukuni na biyu na mata matukan jirgin sama a Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin. A watan Mayu, matar mai shekaru 82 ta koma sararin samaniya wato tukin jirgi, bayan shekaru 31, domin karfafawa ‘yan mata gwiwar shigar masana’antar sufurin jiragen sama.

A ranar 28 ga watan Mayun 2019, Miao Xiaohong, ta tuka jirgin Tecnam P2010, wanda ya tashi daga filin jirgin saman Pinggu Shifosi na Beijing. Yayin tafiyar mintuna 40, sai da ta rera waka mafi soyuwa a gare ta, mai taken “Ina kaunar sararin samaniya na kasata”.

Bayan jirgin ya sauka lami lafiya, Miao ta ce ta ji dadin sake tuka jirgi, musammam a shekarunta na tsufa. Ta ce, “ babu dadi, dole na bar tukin jirgi da na kai shekaru 50. Na ji dadin sake tuki bayan shekaru 31”.

“Bambancin tukin na yau shi ne, a yau buri na shi ne in more tafiyar. Babu wani aiki da zan yi, kuma ban ji wata takura ba. na yi tuki, na kalli sararin samaniya da gajimare a kewayen jirgin, na kuma more yanayi mai matukar kyau. Na ji dadi sosai!”

An haifi Miao ne a gidan iyalai matalauta a yankin Linqu, dake gabashin lardin Shandong, a watan Afrilun 1937. Kuma ta girma ne a gidan innarta a Ji’nan, babban birnin lardin Shandong. Sannan ta kasance mai hazaka a makaranta.

Kasar Sin ta fara horar da rukuni na farko na mata masu tuka jirgi ne a 1951. Kuma a 1956 ne Miao ta shiga cikin rukuni na biyu na mata matukan jirgin sama, bayan ta kammala horo mai tsanani.

“Wata rana a watan Afrilun 1956, ina karatu a makarantar midil mai lamba 3 a lardin Ji’nan. Hafsoshin sojin sama da dama suka zo makarantarmu don horar da masu tukin jirgin sama. Baki daya makarantar ta hargitse, dalibai suna ta sanya sunansu daya bayan daya”, in ji Miao. Duk da sirantakarta, ta sanya sunanta. “Abin alfahari ne a ce mace ta tuka jirgin sama, kuma ba da gudunmuwa ga kasarta. Dole na kokarta”.

Abun mamaki, ita kadai rudunar sojin saman ta dauka daga makarantarsu. A wannan shekarar, dalibai 8 kawai aka dauka daga lardin Shandong.

Sai dai, Baban Miao bai fahimta ko goyon bayan matakin da ta dauka na zama mai tukin jirgin sama ba. “Ina da kwazo sosai a makaranta a lokacin, kuma babana yana son in zama Injiniya ko kwararriya a fannin kimiyya,” a cewar Miao. Duk da rashin amincewar babanta, Miao ta dau Jakarta, ta bar gida, ta fara rayuwarta a matsayin mai tukin jirgin sama.

watan Yunin 1956, aka dauki Miao a makarantar share fagen koyon tukin jirgi, domin samun horon motsa jiki da na soji. Tsanani da wahalar horon, ya zarce abun da Miao ta tsammata. “Kalubale ne ga ko wace mace dake karbar horo. Bayan shafe yini guda ana karbar horo, kafafuna suka min nauyi, motsa su zuwa gado ya zama abu mai wahala.” a cewar Miao. A wannan lokacin, an kori dalibai da dama daga shirin.

Bayan rabin shekara, sai aka mayar da Miao makarantar koyon tuki, daga nan ta fara koyon tuka jirgin sama. A ranar 1 ga watan Afrilun 1958, Miao ta fara tuka jirgi a karon farko a rayuwarta. Sai dai, fiffiken jirgi ya lalace sakamakon kuskuren da Miao ta yi lokacin da ta yi kokarin sauke jirgin. “Na ji kunya, kuma na kasa ma fita daga jirgin a lokacin”, a cewar Miao.

Wannan hadarin ya takura Miao sosai. “Wata daga cikin rukuni na farko na mata masu tuka jirgin sama ta ce min, ba zan taba zama mai tukin jirgin sama ba, idan na ki sake tuka jirgi.” Saboda taimako da shawararta, Miao ta yi karfin hali, ta yi bitar dabarun tuka jirgi, daga bisani ta tuka kanta ita kadai.

Ta kammala makarantar koyon tukin jirgin sama a karshen 1958. A shekarun da suka biyo baya, ta gudanar da ayyuka masu muhimmanci, ciki har da jigilar kayayyakin agaji, kuma ta fuskanci yanayi masu hadari.

A shekarar 1963, Miao ta gudanar da aikin sauke kayayyaki daga jirgi ba tare da sauka ba, a wani wuri da ambaliyar ruwa ta aukawa a lardin Hebei na arewacin kasar Sin. Sai dai rashin iya ganin hanya da kyau ya hana ta gane wuraren da za ta sauke kayayyakin domin gajimaren sun kai kimanin mita 100 daga ban kasa. Amma hazakarta ta sa ta gudanar da aikin cikin nasara.

“Bisa doka, mace mai tukin jirgi za ta daina aiki idan ta kai shekaru 50, kuma na daina da na kai shekaru 51, a shekarar 1988. Zancen gaskiya, ban yi shirin dainawa ba”, a cewar Miao. “Na taba karanta wani rahoto a kan wata Ba’amurkiya mai tukin jirgi, wadda ta shiga gasar tukin jirgi tana da shekaru 80. Da alama babu ruwan tukin jirgi da shekaru.”

A shekarar 1989, Miao ta yi ritaya ta fara rubutu. Bisa kwarin gwiwar da mijinta He Xiaoming ya ba ta, Miao ta fara rubuta tarihinta, da ta yi wa lakabi da “Diyar sararin samaniya”.

Ga mamakinta, littafin nata ya samu karbuwa kuma wannan ne ya ba ta damar sake rubuta wani littafin, mai suna “Rukuni na farko na mata masu tukin jirgi na kasar Sin”.

“Wannan rukunin sun sha wahala sosai, kuma irin kwarin gwiwarsu abun koyi ne”, a cewar Miao. Yayin da take rubuta littafin, Miao ta karye a kafarta ta dama, kuma ta dade ba ta iya motsawa. Mijinta He ne ya maye gurbinta, inda ya ziyarci rukuni na farko na mata matukan jirgin sama, wadanda ke zaune a yankuna daban daban na kasar Sin. He ya tattaro abubuwa da dama ya kai wa matarsa. An wallafa littafin ne a shekarar 2011.

Gogewar da ta samu a rubutun ya fadada tunanin Miao. “Duk da cewa ba zan iya tukin jirgin sama ba, zan iya amfani da alkalami in rubuta da yada labarai da kwazon mata masu tukin jirgin sama,” a cewar Miao.

Shekaru 3 da suka gabata, ita da mijinta suka fara shirin rubuta littafi a kan tarihin shigar mata aikin raya bangaren sufurin jiragen sama na farko- farko a kasar Sin da ma ketare.

Yayin da Miao take bincike a littattafai, ta gano cewa, mata da dama da suka manyanta a wasu kasashen, suna tuka jirgin sama, sai ta yanke shawarar tana son komawa tuki.

Yayin wata liyafa gabanin Bikin Bazara ta 2019, Miao ta bada labarin wani mutumin Faransa da ya manyanta, wanda ya fara tuka jirgin sama lokacin da yake da shekaru 80.

“Yar uwa, ke ma kin iya tukin jirgi!” Liu Fengyun, daya daga cikin rukuni na 4 na mata masu tukin jirgi ne ta fadawa Miao haka yayin liyafar.

Abun da ya fi damun Miao shi ne, ko yanayin jikinta zai bar ta ta sake tuki. “Na karye a duka kafafuna kuma na ji ciwo sosai a hannuna”.

A karshe, ta yanke shawarar tinkarar kalubalen. Domin shirya tukin jirgi a watan Mayu, Miao ta tsara horo. Ta kan taka a kafarta har sau 3,000 a ko wace rana, kuma tana motsa hannaye da kafafunta domin cimma abun da ake bukata na tuki.

Ta ce ta damu sosai saboda shekarunta sun kai 81, kuma saboda ta kai shekaru 31 ba ta tuka jirgi ba. Amma da ta zauna a kujerar tukin a ranar 28 ga watan Mayu, ta samu nutsuwar kammala aikin. Miao ta kammala tafiyar minti 40 ne bisa rakiyar mai ba ta horo.

Bayan ta kammala, ta yi farin ciki sosai kamar wata ‘yar karamar yarinya. Ta ce, “burina shi ne in koma tukin jirgi”.

“Muna da mata masu tukin jirgin sama da jirgi mai saukar ungulu da na jiragen yaki da ‘yan sama jannati. Hanyar zuwa sararin samaniya, na kara fadada ga mata. Ina fatan karin ‘yan mata za su shiga masana’antar sufurin jiragen sama.”

“Shekaruna 82 kuma na sake tuka jirgi. Ku, matasa, za ku fi ni iyawa. Idan kasata na bukatar in tuka jirgi, zan so in tuka” cewar Miao.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: