Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Yawancin Kasashen Duniya Sun Amince Da Matsayar Kasar Sin Daya Tak A Duniya

Published

on

Yau Jumma’a kasar Kiribati dake kan tsibirin tekun Pasifik, ta sanar da cewa, ta riga ta yanke huldar diplomasiyya da hukumar Taiwan. Kasar ta kasance kasa ta biyu wadda ta yanke huldar diplomasiyya da hukumar Taiwan a cikin mako guda, bayan kasar tsibirin Solomon Islands dake kan tsibirin tekun Pasifik ta kudu. Kawo yanzu kasashen dake da huldar diplomasiyya ta kai tsaye da hukumar Taiwan ba su wuce 15 kacal ba.
Hakika muhimmin kudurin da kasashen nan biyu wato Kiribati da Solomon Islands suka tsaida, ya dace da yanayin kasa da kasa da ake ciki, haka kuma ya dace da ra’ayin al’ammun kasashen duniya, ya kuma shaida cewa, yawancin kasashen duniya suna nacewa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya.
A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, hukumar Taiwan tana gudanar da harkokin wajen yankin ta hanyar yin amfani da kudi a fadin duniya, lamarin da ya kawo rashin zaman karko ga wasu kasashe da yankunan da abun ya shafa. Yanzu haka dai an kara fahimta cewa, hukumar Taiwan ba ta so ta taimakawa kasashe da yankunan da abun ya shafa, inda take son cimma kudurin ta na samuwar “kasar Sin guda biyu”, ko “kasar Sin daya da Taiwan daya”.
An ce, hukumar Taiwan ta riga ta tsaida kuduri cewa, za ta janye tawagogin kwararru a fannin fasahohi, da tawagogin likitoci da ta tura wa Solomon Islands, lamarin da ya nuna cewa, hukumar Taiwan ba ta da sahihanci ko kadan.
Kawo yanzu, gaba daya adadin kasashen duniya wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin bisa tushen ka’idar kasar Sin daya tak a duniya ya riga ya kai 178, a don haka kasar Sin tana sa ran cewa, hukumar Taiwan za ta kara gano hakikanin yanayin da ake ciki yanzu, ta tsaida kudurin da ya dace a hankali, in ba haka ba kuwa, za ta ci gaba da gamuwa da matsala kamar yadda take fuskanta a yanzu.

(Mai Fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: