Connect with us

Uncategorized

Hattara Iyaye: Mu Kula Da Tarbiyyar Yaranmu

Published

on

Mutane masu mataccciyar zuciya marasa tsoron Allah, domin za ka ga wasu dattijai ne, wasu kuma matasa ne, sai ka ga an sami dattijo dan shekara 40 ko ma 50 ya kama yarinyar da ba ta shige shekaru 2, 3, ko 4 ba yana mata fyade. Wannan sai dai mu ce Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Wannan kuma kalubale ne a gare mu mu iyaye maza sannan kuma kalubale ne ga iyayenmu mata, domin namiji zai fito ya bar yaran nan tare da iyayensu mata, su ne masu kula da tarbiyarsu. Wannan tsokacin ya fito ne daga bakin Alhaji Husaini Adamu Yakun, shugaban masu siyar da Kaji da kwai na Jihar Kaduna, a lokacin da yake tsokaci a kan yawaitar annobar masu yi wa kananan yara fyade.

Yakun ya ci gaba da cewa, “Sau da yawa irin wadannan tsaffin najadun sukan yaudari yara ne da ‘yar alawa, kamar sweet din nan na naira biyar-biyar, ko biskit na naira goma-goma. Iyaye na kallo sabili da abin da za a iya kira da kawaicin banza na wasu iyayen, suna ganin dan wannan sweet da dattijon banzan nan ya baiwa yarinyar nan kamar kauna ce, ba cewa ake ba a kyauta ba, amma yanzun zamanin ne ya gurbace, sau tari ana yin irin wadannan kyautukan ga yara ba wai domin Allah ba ne.

Sau da yawa wasu sun hadu ne da irin mugayen bokayen nan, wadanda za su ba su wai neman sa’a da yin hakan, domin neman wani abin Duniya. Wanda sukan manta da idan ma ka sami Duniyar ina zaka je ne, wasu kuma masifa ce kawai da jarabta. A nan ina kara jan hankalin iyaye musamman mata da su rika sanya kula sosai, hatta kananun yara da ake hada su da na gaba da su yara domin su kai su makaranta, a nuna masu ka da su kuskura wani ya ja hankalinsu, su tabbatar da suna kulawa da su idan kuma sun taso makarantar a riko hannunsu a kawo su gida.

Ranar kuma da babu makarantar a kula da su a lura da yaran ma da suke yin wasa tare da su. Ina kuma jan hankali ga iyaye maza, wannan dan abin da zaka siya in zaka shiga gida na oyoyo baba, kar a raina shi, ka kasance kana siya a kowane lokaci ka dawo zaka shiga gida wanda yaranka suka saba da shi. Domin idan sun saba da wannan abin babu wani da zai zo ya rude su da sweet din naira goma, tunda wannan abin ba sabon abu ne ba a wajen su. Masu kuma irin wadannan dabi’u idan masu shiryuwa ne Allah Ya shirye su, idan kuma ba masu shiryuwa ne ba, Allah kai ka san yanda zaka yi da su, Ka shiga tsakanin mu da su Ya Allah.

Amma dai su ji tsoron Allah, domin wannan yarinyar da ka lalata ba zaka so ka ga an lalata diyarka ba, domin ita ma diyar wanice, wannan yarinyar kana gani watarana za ta zama matar wani, ba kuma zaka so a lalata matarka ba, kana kallo a watarana wannan yarinyar za ta zama uwar wani, ba kuma zaka so a yi wannan fasadin da Uwarka ba. Mu kuma tuna fa za mu koma ga Allah, duk kuma abin da mutum ya aikata zai sadu da Allah, in alheri, mutum zai taras da alherin, in kuma sharri, wa’iyazu billahi, za a taras da sharrin. Allah ka yi mana gam-da-katar da alherin.

Muna kuma yabawa tare da bayar da goyon baya a kan irin tsauraran matakan da gwamnati ke dauka a kan masu aikata irin wannan barnar. Baccin shari’a da yadda take tafiya ne ba, ai da sai mu ce in an kama masu aikata irin wannan abin a kashe su ne, domin in an kashe su an rage mugun iri ne. Don haka muna kara yin kira ga gwamnati da ta jajirce ta kara tsaurara doka a kan masu aikata irin wannan fasadin. 
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: