Connect with us

NAZARI

Rashin Samun Muhadiman Da Za Su Yi Magana Da Yawun Gwamantin Tarayya Ke Cutar Da Gwamnatin Buhari, In ji Farfesa

Published

on

Dakta  Haruna Yakubu Ja’e sanannen Malami ne a Jami’ar KASU mallakar gwamnatin jihar kaduna, a hirarsa da wakilinmu Abubakar Abba, a jami’ar kwararren malamin a fannin ilimin siyasa ya tabo abubuwa da dama da suka hada da, shirin Ruga, baiwa mata mukamai a siyasance da sauran su.

A kwanukan baya ne Shugaba Buhari ya rantsar da ministocin, amma har yanzu wasu yan Nijeriya na ganin ya sake mayar da mata saniyar ware wajen nadasu mukaman minista, musamman ganin sun taka muhimmiyar rawa wajen sake lashe zaben sa a 2019, inda kama ma ya yi ya basu mukamai maau tsuka, shin kaima kana cikin masu irin wannan ra’ayi?

Mata zasu ja ba ‘a basu  kaso mai  tsuka ba, inka kirgasu zakaga basu wuce bakwai zuwa takwas ba kuma mata suna da yawa a Nijeeiya, sannan juma sun bayar da gydunmawa wajen zabe, suna ganin kuma sunfi kowa fitowa wajen kada kuri’unsu. Domin ina ana zabe, zakaga mata sun fito sosai donsu kada kuri’unau. Toh, an basu mukamai kamar takwas dole ne su raina abinda aka basu, wannan kam gaskiya ne, amma a tsari irin namu na Afirka, ya kamata muma muyi koyi da abinda turawa sukeyi, domin zakaga a nan ba irin na turawa muke yi ba, kida ma matan ne da sukayi karatu suka kuma shiga siyasa kuma zasu iya yin shugabanci, saboda haka wannan ba zai zama wani abu ba, zasu dinga gani kamar ana kyararsu. Idan ka kalki yadda siyasar Afrika take, ina ganin ba zai kara wani abu ba in an nada su ko kuma in ba’a nada su ba. Sai dai, a tsarin siyasa ya kamata dinga yi da su.

Wasu na ganin wasu ministocin da ya yi aiki dasu a zangon farko na mulkinsa basu tabuka komai ba, amma ya sake dawo dasu, baka ganin wannan nakasu ne ga mulkin dimokaradiyya?

A siyasance, an baiwa shugaban kasa dama ya nada wanda yake so kuma a yadda yake su ya yi. Amma idan ka duba ba yanzu aka faraba, wani lokacin baya ma anyi haka dinga yi, Nijeriya ta saba da yin hakan, yau inka sauka daga mukamin gwamna inka gama shekaru takwas sai in koma in nemi mukamin Sanata, in na gama sai in dawo a bani minista, haka abin yake su suke zazzagaywa da , itabkanta Majalisar yanzu inka dube ta zakaga Sanatoci wadanda yawanci sun sauka daga mukamin gwamna ne suka dawo, ko kuma sun sauka daga mukamin minista suka dawo, haka dai abun yake. Misali, Fashola, Ngige da Amechie. A dimokiradiyya ba haka akeso ba ana son a saka matasa su shiga, inka kalli wadanda aka dana baji daya wadanda aka haifa ne a daga shekarar 1950 zuwa 1960, shi Malam Pantami shine wanda aka haifa a 195, sauran duk dattawa ne, hakan ne ya sanya matasa suke ganin ba’a sabya su a ciki ba. Amma duk da hakan dai, fatan mu Allah yasa hakan ya haifarwa da Nijeriya alheri, tunda ba shekaru bane wani lokacin ke sanyawa aga aijin ba, kwarewar da mutume suka sake da ita ya kamata a kalla. Kuma inka lura, wasu da aka dawo dasu an kyautata gwanda da aka dawo dasu, misali, Jeofery Inyema  Ministan harkokin waje, kaga ya yi kokari sosai an dawo dashi, Malam Adamu Adamu ya yi ministan ili an kuma dawo dashi a kan mukamin nasa na Ministan Ilimi sunyi kokari sosai,  Fashola ma ya yi ministan jihar Legas har na tsawon shekaru takwas aka kuma bashi ministan ma’aikatar wutar kantarki, ayyuka da gidaje, shima an sake dawo dashi a kan mukamnin na ministan wutar,  ba laifi ya tabuka, Lai Mohammed ya rike mukamninnministan ma’aikatar sadarwa da al’adu, an kuma sake dawowa dashi a kan mukamnin, shi dai muna son da an chanza shi a samu wanda yafi shi baki don gwamnatin abinda ke cutar da ita shine yin magana, babu masu yi mata magana sosai, ba kamar tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ba, inka duba a wancan lokacin tsohon ministan yada labarai Labaran Maku kaga ya yi kokari sosai, ko ina da anyi abu zakaga ya fito ya yi magana, amma Lai yanzu baya magana sosai ba kamar yadda ya yi a lokacin yakinnneman zabe a 2015 ba.

Wacce shawara zaka baiwa Ministocin?

Fatan mu a kullum, Allah yasa nada su ya haifarwa da Nijeriya da mai ido, kar suje su dinga sata da wawura, su dinga yin abin kunya. Sannan kuma suje su dage su shirya kasafin kudi ma’aikatun su da ban-da-ban da wuri tunda waccan gwambatin data shude anyi ta yin korafi a kan jinkirin  kasafin kudi ba’a yin kasafin kudi a kan lokaci a turawa Majalisa da kuma kai ruwa rkna da aka dinga yi a wannan lokacin a kan kasafin kudi tsakanin bangaren zartarwa da majalsar. Yanzu ga alamu, majalisar ta shirya su ake jira su kawo domin inka duba lokaci ya kore shekarar ta riga ta tafi. Wani abu da ya birge ni, a kan ministocin nan shine, sabuwar hukumar da aka bude a Zamfara ta kula da matsalolin tashin-tashina kamar na rikicin yan kungiyar Boko Haram, annobar ambaliyar ruwa. Sai dai kuma na dauka za’a kirkiro da ma’akatar harkokin Fulani, kuma musamman yan Nijeriya, akwai abubuwa uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauko ya kuma watsar dasu, kamar shirin Ruga ance gwamnatin ta ture shi, toh ya kamata ta tabbatar da ta gudanar dashi. Akwai kuma maganar hana Almajiranci da ya kamata ace yara suna zuwa makaranta suna kuma da abincin da zasuci, amma an barsu suna zuwa bara, wannan yawon kaskanci ne. Shima wannanshirinbya kamata aci gaba dashi. Akwai kuma maganar yashe Kogin Neja, domin in har wannan lokacin ya wuce ba’a yi ba, toh banyi tunanin akwai wata gwamnatu da in tazo zata yi ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: