Connect with us

LABARAI

An Bizne Tsohon Shugaban Tunusiya A Kasar Saudiyya

Published

on

Rahotanni dake fitowa daga kasar Saudiyya sun nuna cewa an bizne hambararen tsohon shugaban kasar Tunusiya, Zine Abidine Ben Ali, a ranar Asabar a kasar Saudiyya. Tsohon shugaban kasar wanda yake zaune a Saudiyya bayan mafakar siyasa da ta ba shi, ya rasu ne a ranar Alhamis.

Lauya Mounir Ben Salha ya tabbatar da biznewar da aka yi tsohon shugaban. Ben Ali ya shekara 83 kafin ya bar duniya, inda aka bizne shi a birnin Madina.

Ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiyar da ba a bayyana kowacce iri ba ce. Tun bayan isar sa kasar Saudiyya a watan Janairun 2011 tare da iyalinsa, bai cika bayyana ana ganinsa ba.

Ben Ali ya kwashe shekara 23 yana mulkin kasar Tunisiya. Inda a yayin mulkinsa aka zarge shi da take hakkin bil’adama da kuma mulkin mallaka.

Sakamakon hambare shi da aka yi ya haifar da juyin juya hali a kasashen Larabawa da ya hada da; Misra, Libya da Yemen.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: