Connect with us

MANYAN LABARAI

Buhari Ya Tafi Taron Majalisar Dinkin Duniya A Kasar Amurka

Published

on

A yau Lahadi ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya kama hanyarsa zuwa birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 74. Ana ganin cewa wannan taron da shugaban kasar zai halarta na da matukar muhimmanci ga Nijeriyar ganin cewa an zabi dan Nijeriya wato Tijjani Muhammad Bande a matsayin Shugaban Babban Zauren Majalisar. A kwanakin baya ne dai aka zabi Farfesa Tijjani Muhammad Bande a matsayin shugaban.

Maudu’in da za a tattauna a zauren shi ne ”Fargar da kasashe wajen yaki da talauci da samar da ingantaccen ilimi da kuma daukar matakai kan sauyin yanayi. Za a fara tafka muhawara a zauren ne a ranar Talata 24 ga watan Satumba a inda shugabanni za su yi jawabai game da kasashensu, kazalika za su yi bayanai kan maudu’in taron na wannan shekara. Ana sa ran Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari shi ne mai magana na biyar a wurin taron.

Wannan ne karo na biyu da Nijeriya ke samun gurbin shugabanci a Babban Zauren Majalisar Duniya, inda a shekarar 1989, Manjo Janar Joseph Garba ya zama shugaba. Ana sa ran Shugaba Buhari zai mayar da hankali ne wajen bayani kan ci gaban da ya samu musamman ta bangaren alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zaben 2015 da kuma 2019.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: