Connect with us

LABARAI

Kungiyar MFAN Za Ta Horas Da Matasa Dubu 300 Noman Zogale

Published

on

Hadakar kungiyar manoman zogale da masu cinikayyarta ta Nijeriya wacce aka fi sani da MFAN a takaice, ta bayyana shirinta na horas da matasa dubu 300 yadda ake noman zogale a wani shirinta na magance matsalar rashin aikin yi a Nijeriya.

Shugaban kungiyar, Michael Ashimashiga shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi.

Ashimashiga ya tabbatar da cewa za su horas da matasa 500 ne a cikin kananan hukumomi 774 da ake da su a Nijeriya. Inda ya ce noman zogale yana da riba sosai, kuma ana da bukatarsa cikin kasa da kasuwar duniya.

Ya ce al’umma na bukatar zogale saboda amfaninsa. Ashimashiga ya kara da cewa; za su noma zogalen ne a gona da fadin girmanta ya kai Hekta dubu 10 a jihar Nasarawa nan da wadansu makonni masu zuwa. A cewarsa duk wanda ya amfana da wannan horaswar, za a bashi filin da zai yi noman zogalen, da kuma iri na ba tare da an karbi kudi daga hannunsa ba.

Ya tabbatar da cewa; bayan sun kaddamar da shirin na su, kowanne Kodineta na kowanne karamar hukuma zai je ya horas da matasa 500 a karamar hukumar da yake. Ya tabbatar da cewa; duk wanda ya yi noman, kungiyar ta su a shirye take ta siya abin da ya noma, domin a cewarsa ana da bukatarsa a kasuwanni.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: