Connect with us

KASUWANCI

Sirrin Kasuwancin Dangote Guda Bakwai

Published

on

Kasancewar sa mamallakin kamfanin Dangote da ke samar da kayayyakin masarufi iri-iri a Najeriya da wasu kasashen Afirka ba wasa ba ne. An kiyasta yawan dukiyar Dangote ta kai Dalar Amurka biliyan 12.5 yayin da mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka kuma na 67 a jerin masu kudin duniya.

Duba ka ga wadansu hanyoyi da ya nuna su ne makasudin nasararsa ga wadanda su ke son zama kamarsa:

1. Tsayawa wuri daya. Babban attajirin ya shawarci ‘yan Najeria su dinga tsayawa guri daya a duk abin da su ke yi. Tsallen badake daga waccan sana’a zuwa wannan ba tare da cin nasara ba, ba abu ne mai kyau ba.

2. Sauraron jama’a. Daya daga cikin mabudan nasarar Dangote da ya fada da bakinsa ga masu son cin nasara a rayuwa, shi ne sauraro. Dole ne ka saurari jama’a kuma ka tsaya ka koya a wajensu, hakan zai taimaka ma ka samun ilimi daga bangarori daban-daban.

3. Hangen nesa kokarin samun nasara ba ta lokaci ne, in har ba ka da hangen nesa.

4. Me za ka yi? A wace irin harka za ka samu nasara?

5. Mai da hankali. Dangote bai ta ba yin wata harka da ba shi da ilimi a kanta ba. Aliko Dangote ya bayyana wannan a daya daga cikin hanyoyin samun nasararsa ma fi amfani. Ka gujewa duk wani abu da zai dauke ma hankali daga harkokinka.

6. Ka samu sahihan bayanai, Tsunduma cikin harka ba tare da saninta ba, ba abu ne da zai haifar da da mai ido ba. Dangote ya ce, bai taba shiga wata harka ba, ba tare da ya samu sahihan bayanai game da ita ba. Ka da ka yanke gurguwar shawara saboda rashin sani.

7. Zuzzurfan tunani. Yin zuzzurafan tunani ba zai zama matsala ba tun da ba zai sa ka asara ba. A cewar Dangote kwakwalwarka daya ce, kuma ya rage na ka ka fadada tunani, ko ka kuntata shi. Ba wanda ya ke biyan kudi don ya yi zuzzurfan tunani. Bai kamata ka takaice kanka da dan abin da ka sani ba.
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

labarai

%d bloggers like this: