Connect with us

LABARAI

‘Fiye Da Naira Biliyan 470 Ne Suka Shigo Lalitar Jihar Bauchi A Shekaru Hudun Gwamna M. A.’

Published

on

Zunzurutun kudade da suka tasarma naira biliyan dari hudu da saba’in da daya, da miliyan saba’in da uku da naira dubu dari tara da da saba’in da biyar da dari tara da sittin da shida, da kwabo shida suka shigowa lalitar jihar Bauchi a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2019 karkashin jagorancin tsohon gwamna, Muhammad Abubakar na jam’iyyar APC.

Kudaden da suka shigo lalitar, kamar yadda kwamitin zakulo kudade da kadarorin jihar Bauchi suka sulale ya zayyana, sun hada da kudaden shogowa na rabon arzikin kasa na wata-wata da suka kai kimanin naira biliyan dari uku da ashirin da daya, da miliyan dari hudu da sittin, da dubu dari bakwai da hamsin da tara, da naira dari takwas da talatin da kwabo talatin da hudu (N321,460,759,830 34) da basussukan banki na naira biliyan hamsin da takwas, da miliyan dari shida da biyu, da dubu dari uku da tamanin da biyar, da naira dari biyar da arba’in da hudu (N58, 602, 385, 544) a cikin wadannan shekaru hudu na baya.

Mai magagana da yawun kwamitin, Alhaji Umar Barau Ningi ya gabatar da sauran kudaden da suka shigo lalitar kamar haka, naira biliyan takwas, da miliyan dari shida da tara, da naira dubu dari; da naira biliyan biyar da dubu dari tara da da sittin da takwas, da dubu dari hudu da naira cas’in, da kuma naira miliyan dari bakwai da suka kasance bashin ajo daga gwamnatin tarayya wadanda aka baiwa Bauchi a shekaru na 2016, 2017, da 2018 wa gwamnatin Abubakar.

Alhaji Umar Ningi ya shaidawa taron ‘yan jarida a garin Bauchi cewar, a lokacin gwamnatin da ta gabata, jihar Bauchi ta samu rarar kudade daga Faris-kulob na kimanin naira biliyan arba’in da bakwai, da miliyan dari uku da goma sha hudu, da dubu dari uku da talatin da naira dari biyar da daya, da kwabo saba’in da biyu (N47, 314, 330, 501 .72 kamar yadda yadda ofishin babban Akanta na jiha ya gabatar.

A cewar shi; “Sannan kuma, Bauchi ta samu wasu kudade da yawansu ya kai N10,000,000,000 na rancen Edcess Crude, sannan kuma wasu adadin kudade na tallafin kasafin kudi da yawansu ya kai N17, 569, 000, 000daga ofishin babban Akanta Janar na kasa, da kuma wasu kudade N12, 125, 000, 000  daga asusun bayar da lamuni na jihar Bauchi,” A cewar kwamitin.

Alhaji Umar Ningi ya kuma shaida cewar a tsakanin wa’adin mulkin M.A na shekaru hudun an wawushe naira biliyan biyu da digo biyar daga cikin kason karo-karo na albashin ma’aikata.

Kwamitin ya bayyana gwamnatin M.A a matsayin gwamnatin da ta yi wadaka da dukiyar jama’an jihar Bauchi a lokacin da suke karagamar mulki, kwamitin ya ce zai tabbatar da dawo wa jama’an jihar sisi da kwabonsu da aka sace musu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: