Connect with us

LABARAI

Karin Haraji Zai Fi Shafar Masu Kudi -Ministan Kudi

Published

on

Ministar Kudi da tsare-tsaren Bajet, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa kudurin na gwamnatin tarayya na karin kudin haraji zai fi shafar masu kudi ne da kuma mutanen da suke zaune cikin birane.

Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ne a wani taro kan tattalin arzikin Nijeriya karo na 25 da ya gudana a birnin tarayya Abuja a ranar Litinin. Inda ta yi karin bayani da cewa; karin harajin ba zai shafi Talakawa ba kamar yadda ake kokarin nunawa.

A cewar Zainab Ahmed, ma’aikatarta ta yi tsari da Bankin kasa wato CBN kan yadda tsarin karbar kudin zai kasance da kuma kokarin ganin karin karbar harajin ya kawo ci gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: