Connect with us

LABARAI

Attajirai Ku Tsamo Talaka Daga Talauci – Buhari

Published

on

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga ’yan Nijeriya attajirai da su duba yiwuwar bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyar mai da hankali wajen kirkiro sana’o’i, bunkasa harkokin kasuwanci, cinikayya da gina kasa Nijeriya ta hanyar yin amfani da arzikin da Allah ya yi wa kasar, domin tsamo talaka daga tsananin talauci.
Buhari ya yi wannan kira ne a taron Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa karo ta 25 (NES25) da a ke yi a Abuja a ranar Litinin 7 ga Oktoba, 2019. Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da aiki da kamfanoni masu zaman kansu, domin bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma tsara manufofi na cigaba a Najeriya.
Bayan nan sai ya yaba da yadda a ka gudanar da zabukan 2019 da kuma yadda wadanda ba su yi nasara ba su ka garzaya kotu domin kai kukansu. Buhari ya ce hakan na nuna cewa lallai an samu cigaba matuka a harkar siyasa da dimukradiyya a Nijeriya.
“An sanar da ni cewa taron na wannan shekara zai mai da hankali ne wajen tsara hanyoyin da za su samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya, musamman harkokin noma, hako ma’adinai, fasaha da kere-kere da kuma ayyukan zamani na kwamfuta.
“A tattaunawar da muhawarar da kwararru za su yi a wannan taro, Ina son na yi kira gare ku da ku maida hankali wajen tsara hanyoyin da za a samu nasara ne a harkokin samun cigaba da bunkasa tattalin arzikin kasa ta yadda Najeriya za ta amfana da su.”
Bayan haka sai Buhari ya yi tsokaci a kan nasarorin da a ka samu a siyasar Najeriya da zabukan 2019.
“An yi zabuka kuma an kammala su lafiya, Najeriya ta nuna wa duniya cewa za ta iya zaben shugabanninta ba tare da an samu matsala ba. Duk da dai an dan samu ‘yan matsaloli, ‘yan Najeriya sun yi zabuka cikin kwanciyan hankali da lumana.
“Mun ga yadda wadanda su ka fadi zabuka su ka garzaya kotu, maimakon yadda za ka ga an barke da rikice-rikice.
“Tun a can farko, Jam’iyyar mu ta APC ta fayyace manufofin ta karara ga ‘yan Najeriya, da su ka hada da samar da ayyukan yi ga dimbin matasan mu, kakkafa matakai da manufofi masu inganci domin ci gaba a kasar nan.
“Sai dai kash wasu da dama basu fahimci abinda muke nufi da haka ba wasu na ganin.
“Najeriya kasa ce da ke da al’umma kusan miliyan 200 a cikin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja. Mafi yawan arzikin kasar ya na dankare ne a wasu jihohin da ba su wuce hudu ko biyar ba tare da babban birnin tarayya. Wasu daga cikin attajiran kasar nan na zaune a cikin wannan dakin kuma sun sani.
“A haka kenan jihohi 31 dake da mutane akalla miliyan 150 na zaman hannu baka hannu akushe ne da ya sa a yanzu kasa ke ta fama da matsalolin tsaro da yaki ci yaki cinyewa. Hakan ya sa kasashen da ke kewaye da Najeriya na fama da irin wadannan matsaloli.
Buhari ya ce gwamnatin sa za ta maida hankali wajen ganin an tsara manufofin da za su inganta tattalin arzikin kasar nan da kuma samar wa mutane sana’o’i da inganta zamantakewa a tsakanin mutanen Najeriya da tsaro.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: