Connect with us

LABARAI

An Bukaci Kanawa Su Bai Wa Ganduje Goyon Baya Don Cigaban Kano

Published

on

An bayyana nasara da Gwamna Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya samu na sake tabbatar da nasarar zabensa karo na biyu da cewa dorewar cigaba ne a jihar, Dakta Alhaji Sani Muhammad Tsamiya Babba Sarkin shinfida na masu maganin gargajiya na jihar Kano ya bayyana haka.

Ya ce, irin ayyuka da Gwamnan yayi a fadin jihar nan shi yasa mutane sukaga cancantar su sake zabarsa a karo na biyu kuma suka zabe shi. Duk da haka saida wasu suka ja har akaje kotu ta raba gardama ta tabbatar da nasara ga Gwamna.

Dokta Sani Muhammad Tsamiya Babba yayi kira ga sauran yan siyasa su zo su hada-kai da Gwamna Ganduje domin a ciyar da jihar Kano gaba  domin kishin Kano shine gaba da komai.

Sarkin shimfidar masu maganin gargajiyar na jihar Kano. Sani Muhammad Tsamiya Babba ya yaba wa Gwamna Ganduje bisa nadin da Sheik Harun Ibn Sinah a matsayin babban kwamanda na Hisbah na jahar Kano domin an sanya cancanta.

Ya ce, Ibn Sinah Mutumne da yake bada gudummuwa sosai wajen cigaban addini wannan matsayi kara masa nauyine na cigaba da yi wa addini hidima wajen umurni da kyakkyawa da hani da mummuna da fatan al’ummar Kano za su bashi hadin-kai.

Sarkin Shinfidar masu maganin gargajiyan na ji har Kano, Dokta Alhaji Sani Muhammad Tsamiya babba ya yabawa Gwamnatin Kano bisa kulawa da take bayarwa wajen inganta sana’ar masu maganin gargajiya ta janyo su a jika dayi musu bita ta yanda za su kyautata sana’arsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: