A makaon da ya gabata ne, hukumar kididdiga ta kasa NBS ya shelanta cewa, fannin aikin noman kasar nan ya kara bunkasa, inda fannin a cewarta, ya habaka da kashi 2.17a cikin 2020.
A cewar hukumar kididdiga ta kasa a cikin shekarar 2019, karin kashi 2.36 aka samu, inda kuma cikin 2018 aka samu karin kashi 2.12 kadai.
Hukumar kididdiga ta kara da cewa, hakan ya nuna a shekarar 2020 an fi shekaru biyu na baya da suka gabata samun albarkar noma kenan.
Bugu da kari, rahoton ya bayyana cewa harkar noma a 2020 ta bunkasa sosai a cikin watanni uku na karshen shekara, inda kuma a wadannan watanni ne tattalin arzikin cikin gida na kasar nan, ya karu da kashi 26.21.
Wannan fita daga matsin tattalin arziki kuwa na da nasaba da bude kofar kullen korona da aka yi wa jama’a na tsawon watanni.
Har ila yau kuma, tattalin arzikin kasar nan ya shiga cikin matsala a cikin watannin shida, bakwai da takwas na shekarar 2020, inda hakan ya janyo kasar nan tsunduma a cikin matsin tattalin arziki da kuncin rayuwa karo na biyu, a cikin shekaru biyar.
Rahotaon ya kara da cewa, tattalin arzikin kasar nan a wancan lokacin ya dan tauye da kashi1.92, fiye da yadda Bankin Bada Lamuni na duniya ya yi has ashen kan kasar nan.
Bugu da kari kuma rahoton ya bayyana cewa, fannin kayan abinci, kiwon dabbobi, kula da dazuka da kuma bunkasa sana’ar kiwon kifaye ne su ka cicciba tattalin arziki a fannin noma har ya samu waraka da nasibi cikin 2020.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, an samu albarkar kayan gona na bangaren abinci sosai a shekarar 2020, daga su kuma sainsana’ar kiwon kifi su ne su ka kara wa fannin noma albarka sosai.
A wata sabuwa kuwa, Bankin Raya Afirka da ake kira AFDB a takaice, na shirin kashe zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan 500 don bunkasa masana’antu na musamman don taimaka wa ci gaban harkar noma a Najeriya.
Baban Darakta a bankin na AFDB Ebrima Faal, ya ce sun bullo da tsarin na bunkasa aikin noma a kasar na ne saboda sassan Afrika da dama suna fitar da muhimman albarkatun kasa zuwa ketare domin a sarrafa su kana a sake dawo da su, yin hakan na kawo kashe kudaden musaya masu yawa a cewarsa.
Bugu da kari, a fannin, Ministan ma’aikatar Noma Alhaji Muhammad Sabo Nanono, ya ce duk kananan hukumomin Najeriya za su samu wannan damar, domin bunkasa harkar noma.
Shi ma babban daraktan hukumar NIRSAL Aliyu Abbati Abdulhameed ya bayyana cewa, babban bankin Nijeriya ya kirkiro da dabarun da za a bunkasa harkar noma da tallafa wa manonan kasar.
Aliyu Abbati Abdulhameed ya kara da cewa, wannan tsarin zai taimaka wa kananan manoma ta yadda za a yi noma a kuma sarrafa kayan gonan duk a wuri daya ba sai an kai kasashen waje ba.