Yusuf Shuaibu" />

2020: Gwamnatin Nijeriya Ta Samu Dala Biliyan 16.74 A Zuba Jari – NIPC

NIPC

NIPC

Hukumar bunkasa jari ta Nijeriya (NIPC) ta bayyaba cewa, gwamnatin tarayya ta samu rabar dala biliyan 16.74 daga bangaren zuba jari. Jimillar yawan kudaden bai kai na shekarar 2019 ba, wanda aka sami dala biliyan 29.91.

Hukumar NIPC ta bayyana hakan ne a taron manema labaran da ta kira a wannan mako a garin Abuja.

Ta bayyana cewa, an samu raguwar kudaden jarin ne sakamakon matsaloli masu yawa da cutar Korona ta haddasa a bangarorin zuba jari a shekarar 2020. Hukumar NIPC ta bayyana cewa, ta samu yawan kudaden a ayyuka 63 a jihohi 63 ciki har da Babban Birnin Tarayya a shekarar 2020. Wanda Jihar Legas ce tafi yawan ayyukan wacce take da guda 24.

A baya dai, Jihar Ribas ce take kan gana ga kowacce jiha wanda aka samu jari na dala biliyan shida, inda Jihar Kaduna ke biye mata da dala biliyan 2.8, sai Jihar Kogi da ke dala biliyan daya da kuma Jihar Legas da ke da dala biliyan 890.

“Bincike ya nuna cewa, an fi samun yawan kudaden jarin a bangaren masana’antu  guda 10, wanda aka samu yawan kudade na dala biliyan 8.4 na kashi 50.

“An dai samu kashi 28 a bangaren harkokin sufuri, yayin da aka samu kashi 11 a sadarwa, an sami kashi shida daga bangaren masana’antu, haka kuma an sami kashi uku daga bangaren kudade da inshore, wanda su ne manya a cikin bangarori guda biyar a wannan shekarar,” in ji NIPC.

NIPC ta kara da cewa, an samu kashi 36 daga asusun kasar Singapore a wannan lokaci, sanan sai kasar China wanda aka samu na kashi 22 da kuma Amurka wanda aka samu na kashi 15. Hukumar ta bayyana cewa, cutar Korona ta yi matukar raunata kudaden zuba jarin a watan Fabrairun shekarar 2020.

Exit mobile version