Daga Umar Faruk,
Hukumar kashe gobara ta jihar Kebbi, a jiya ta sanar da cewa ta samu rahotonnin tashin gobara 173 da ta yi sanadiyar mutuwar mutum daya a shekarar ta 2020.
Daraktan hukumar, Alhaji Yahaya Garba Zazzagawa, ya shaida wa manema labarai a Birnin Kebbi cewa gobarar ta faru ne tsakanin watan Janairu zuwa Disamba shekarar da ta gabata.
“Daga watan Janairu zuwa Disamba a shekarar 2020, mun yi samu rahotonnin tashin gobara 173 da ceto rayuwar mutum daya da kuma daya da ya rasa ransa a tashin gobarar.
Sauran sun hada da watan Yuli tashin gobara 19, sai kuma tashin gobara a watan Augusta 7, Satumba an samu tashin gobara 7, sai watan Oktoba shi ma an samu tashin gobara 7, haka kuma watan Nuwamba an samu tashin gobara 16 daga karshe a watan Disamba an samu tashin gobara 24.
Ya ce “Mutum daya ya rasa ransa a watan Disamba, sai kuma an ceto daya da ransa. An samu raguwar adadin tashin gobara da kuma mutuwar mutane da ke aka rubuce a kundin tarihin tashin gobara na hukumar kashe gobara ta jihar kebbi a shekarar 2019, bisa ga shekarun baya.
“Duk da cewa, mun dauki adadin kididikar gobara 173 sama da na shekarar 2019; amma an samu raguwar mutuwa daga 11 a shekara ta 2019 zuwa guda daya a cikin shekara ta 2020, saboda hukumar ta dauki matakin gudanar da yekuwa da kuma wayar da kan jama’a, kan illolin da hadarin tashin gobara a cikin al’umma, in ji shi Daraktan hukumar da kashin gobara na jihar kebbi Alhaji Yahaya Garba Zazzagawa”.
Zazzagawa ya ce don hana ci gaba da samun barkewar gobara a jihar, ya zama wajibi ga mazauna a ko yaushe su yi taka tsan-tsan wajen amfani da kayan lantarki da sauran abubuwa masu saurin kamawa da wuta don kan a tabbatar da cewa an kashe kayan lantarki a duk lokacin da za a barin gida ko bayan an dauke wutar lantarki.
“Sama da kadarori na sama da Naira Miliyan 240 aka yi asara sakamakon tashin gobarar, da kuma Naira Miliyan 450 na kadarorin da aka adana yayin barkewar gobarar,” inji shi.
Har ila yau, Zazzagawa ya umarci masu shan sigari da su tabbatar cewa ko yaushe basu zubar da sigarin ba , musamman a wuraren da ciyawar take don yana zama sanadiyar tashin gobara kai tsaye. Saboda haka sai an kaucewa zubar da sigari mai wuta a wuraren da bai dace ba, don yana da hadarin gaske.
A cewarsa, hukumar kashe gobara na bukatar samar da karin motocin aiki don saurin magance matsalolin gobara a jihar.
Daga karshe Daraktan ya yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta wadata sashen da abubuwan da zaya karkakawa hukumar wurin gudanar da ayyukan ta yadda ya kamata don saurin amsa kiraye-kiraye tsahi da barkewar gobara a duk fadin jihar.