Connect with us

RA'AYINMU

A Samar Da Manufar Kasa Game Da Ciwon Hanta

Published

on

Nijeriya na cigaba da fuskantar barazana ta fuskar harkar lafiya, yayin da kaso 5% ke dauke da ciwon hanta, wanda kan yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane Milyan biyar a duk shekara a wannan kasa.

Kusan a mafiya yawan Asibitoci, musamman na gwamnati sun fi karancin Likitoci masu kula da wannan ciwo na hanta a fadin wannan kasa, sannan batun daukar Likitocin tare da horar da su don magance wannan matsala, a kullum kara ja baya yake yi.

Har ila yau, bincike ya nuna cewa, kusan ‘yan Nijeriya Milyan 27 ne ke dauke da ciwon hanta. Babban abin tsoro game da wannan cuta kamar yadda Masana ke cewa shi ne, mutane da daman a dauke da wannan cuta ta ciwon hanta amma ba su sani ba, har sai ciwon ya gama cin karfinsu bakidaya. Kazalika, ciwon hanta na haddasa ciwon kansa, ta yadda har lokacin mutuwar mai cutar na iya yi ba tare da bayyana a tare da shi a fili ba.

Haka nan, Masanan sun dora alhakin yawan mace-macen da ake yi sakamakon wannan ciwo na hanta akan Hukumomin kula da kiwon lafiya, gwamnatoci da kuma sauran masu ruwa da tsaki. A cewar tasa (Masana Kiwon lafiya), karancin wayar da kan al’umma akan wannan ciwo na hanta a Nijeriya da kuma bin irin hanyoyin da suka dace, su ne ke kara taimakawa wajen cigaba da yaduwar wannan cuta a tsakanin al’umma, musamman idan aka yi la’akari da yadda ba a damu da yin rikafi ba da sauran makamantansu.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta bayyana wannan cuta a matsayin wadda ke yi wa hanta matukar illa ta kuma lalata ta kwata-kwata. Sannan, tana iya rikidewa ta zama ciwon kansa mai wuyar sha’ani. Don haka, akwai abubuwan da ke haddasa wannan cuta da ya hada da shan giya ko miyagun kwayoyi da sauran makamantansu.

Haka nan, kamar yadda Masana suka bayyana wannan cuta ta hanta kusan kashi hudu ta rabu, akwai A, B, C, D da kuma E. Ko shakka babu, wajibi ne a baiwa wadannan rukunai matukar muhimmanci sakamakon illolin da ke tattare da su da sanadiyyar kisan da suke yi da kuma yaduwar da suke faman yi a tsakanin al’umma. Bugu da kari, rukunin B da C sun fi illa wajen cutarwa, domin kuwa daruruwan Milyoyin ‘yan Nijeriya na dauke da su, wanda kan sauya ya zama ciwon kansa.

Hukumar lafiya ta duniya ta sake bayyana cewa, rukunin A da E na wannan ciwo ta hanta, na samuwa ne sakamakon rashin samun narkewar gurbataccen abinci ko ruwan sha a cikin mutum. Haka nan, rukunin B, C da D na samuwa ne ta hanyar cudanya da juna, musamman a tsakanin ma’aurata da iyali, sanya wa wani jinin mai dauke da wannan ciwo, yin amfani da allura ko wani makamancin haka, yayin da uwa ta zo haihuwar danta ko kuma saduwa tsakanin mace da namiji.

Wani lokaci, alamu kan bayyana wajen gane cewa an kamu da wannan ciwo na hanta, ta hanyar ganin fata ko ido ya yi yalo, canzawar fitsari, yawan yin gumi, tashin zuciya, amai da kuma ciwon jiki.

Kamar yadda Cibiyar kula da cututtuka ta duniya ta bayyana, ana yawan samun mace-mace sakamakon wannan cuta ta hanta fiye da cutar Kanjamau (HIV/AIDS), Maleriya da kuma Tarin-fuka, idan ban da kwana-kwanan nan da aka samu wani cigaba na samun wani magani wanda a cikin watanni uku zai iya warkar da rukunin C tare da samun wadataccen rigakafin rukunin B.

Sannan, bincike ya sake nuna cewa, wannan ciwo na hanta ya fi kashe mutane a duniya fiye da hadarin mota, masu ciwon Asma, masu ciwon zuciya da sauran makamantansu. Don haka, ya zama wajibi mu dauki dukkanin irin matakin da ya dace wajen ganin an yaki wannan ciwo ta ko’ina, musamman ta fuskar yawaita yin gwaji da sauransu.

A duniya kaf, bai fi kaso 5% wadanda suka san cewa na dauke da wannan ciwo na hanta, shi yasa cutar ke cigaba da yaduwa a tsakanin al’umma ba tare da neman magani ba. Kazalika, wasu kuma na samun matsala wajen gwaji, suna da shi watakila a ce da su ba su da shi, wasu kuma bakidaya ma ba sa zuwa gwajin ballantana su san abinda suke ciki, domin daukar matakin da ya dace. Don haka, ya zama tilas Mahukuntan Nijeriya su mayar da hankali akan wannan ciwo na hanta tare da sanya idanu da kuma tabbatar da ganin an yi dukkanin abinda ya dace domin kuwa wannan cuta na da magani.

Rage yawan masu wannan ciwo da kuma mace-macensu zuwa kaso 65 daga nan zuwa shekarar 2030, shi babban abinda Hukumar lafiya ta duniya ta sanya a gaba. Wanda wannan ya hadar da gwamnatoci 194, wadanda suka kudiri aniyar aiwatar da wannan shiri, wanda ake sa ran idan aka samu nasarar aiwatar das hi yadda ya kamata, za a iya kawar da wannan ciwo kwata-kwata daga nan zuwa shekarar 2030.

Shi yasa wannan Gidan Jarida, ya bayyana matukar farin-cikinsa lokacin da Hukumar kokarin kawar da wannan cuta ta hanta ta Nijeriya, ta ziyarci LEADERSHIP a Babbar Shelkwatarta da ke Abuja kwana-kwanan nan, domin yin hadin gwiwa da Kamfanin don cigaba da wayar da ‘yan Nijeriya game da wannan ciwo na hanta da kuma yadda za a magance shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: