Connect with us

LABARAI

An kaddamar Da Kwamitocin Zauren Masalaha A Fagge

Published

on

Shugaban karamar hukumar Fagge.Hon.Ibrahim Muhammad Abdullah Shehi ya kaddamar da zauren masalaha don kyautata zamantakewa da cigaban al’ummar yankin.
Taron da aka gudanar a harabar sakatariyar karamar hukumar ranar Asabar ya sami halartar masu ruwa da tsaki na bangarori daban-daban na al’ummar Fagge.
Da yake jawabi a wajen taron kwamishinan ma’aikatar addini, Dakta Muhammad Tahar Adamu ya ce, Gwamnatin Kano za ta taimakawa wannan yunkuri na Fagge wajen fito da wannan tsarin.
Sannan yaja hankalin ‘yan kwamitin masalahar na Fagge akan karsu danganta wannan tsarin nasu da Gwamnati su tsaya akan abune na al’umma domin hakan zaisa kowa ya tsaya yayi aikin da zai amfani al’umma.
Shima a jawabinsa kwamishinan kananan hukumi Hon. Muttala Sule Garo wanda Sakataren dindindin na ma’aikatar Alhaji Sale Minjibir ya wakilta yaja hankalin sauran kananan hukumomin jihar Kano akan suyi koyi da abinda shugaban karamar hukumar Fagge ya yi ma samatda irin wannan zaure na masalaha dan kyautata da zamantakewa.
A jawabinsa shugaban karamar hukumar Fagge Hon. Ibrahim Muhammad Shehi ya gode wa Allah bisa dama daya bashi wajen yin wannan kwamiti na masalaha a tsakanin al’ummar Fagge.
Sannan yaja hankalin al’umma akan su dubi matsalar saida gidaje da ake a kwaryar Fagge ana mai dasu manyan shaguna da sito-sito da kuma yin manyan shaguna da masu bene da ake hango cikin gidajen mutane sannan ana saida ha gidajen ga mutanen da ba’asan daga inda wasunsu suke ba. Wanda nan gaba in aka bar abin haka sai an rasa ‘yan Fagge a gudanar da harkoki a cikinta.
Hon. Shehi yaja hankalin yan kwamitin na masalaha suyi kokari wajen kawo gyara kuma a matsayinsu na shugabanni za su dan ayi kokarin kawo kariya daga aukuwar hakan.
Sannan ya koka akan matsalar yawan shae-shaye da yawon yara mata daya kamata ayi amfani da wannan masalaha dan kawo gyara dan dakile irin wadannan a tsakanin matasa.
Ya yi kira ga manya masu ruwa da tsaki na Fagge tun daga manyan malaman jami’oi dana addini da yan kasuwa su shigo su baiwa Fagge gudummuwa.
Shehi ya ce, wannan kwamiti na Masalaha ba maganace na siyasa ba wani dandali ne daya hada dukkan al’umnar Fagge kowa ya shigo ya bada gudummuwa don kyautata tarbiyya da cigaban al’umma.
Shima a jawabinsa mai bai wa Gwamna shawara kan addinai Ali Baba Fagge ya bayyana jin dadinsa ga bijiro da zauren na masalaha.
Shima a jawabinsa tsohon kakakin majalisar Kano, Rt. Hon. Yusuf Ata yaja hankalin yan kwamitin su dauka aiki ne za su yi don Allah ba wani abu za’a rika basu ba.
A nasihar da ya gabatar a yayin taron Malam Umar Sani Fagge ya bayyana cewa ita masalaha tafi sulhu dadi domin tana kange duk wata fitina tana hada kan al’umma.
Tun farko a jawabinsa na maraba daraktan mulki na karamar hukumar Fagge Alhaji Ibrahim Umar ya nuna farin cikinsa da cewa taro ne na samar da masalaha wanda kuma mataki ne na samar da aminci tsakanin al-umma kuma ita rayuwa bata wanzuwa saida aminci.
A yayin taron an kaddamarda kwamitin koli na Kwamitin na masalaha a matakin karamar hukumar dake karkashin shugaban karamar hukumar Hon. Shehi sai Hakimi a matsayin mataimaki da sauran shugabanni haka kuma an kaddamar da shugabannin kwamitin na matakin mazabun yankin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: