Connect with us

RAHOTANNI

Dan Majalisar Kano Zai Hana Maza Daukar Hoto Cikin Mata

Published

on

Wakilin al’ummar Karamar Hukumar Tarauni a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Hafiz Ibrahim Kawu, ya dauki nauyin horar da mata ‘yan shekaru 18 sana’ar daukar hoto irin na zamani, domin ya kawo karshen yadda maza ke cakuduwa da mata a lokacin bukukuwa, domin daukar su hotuna.

Wannan kuma na cikin kokarin wakilin al’ummar na sama wa matasa maza da mata sana’o’i, domin dogaro da kawunansu.

Da ya ke gabatar da jawabi a lokacin bikin kaddamar da shirin horar da mata sana’ar daukar hoto, wanda aka gudanar a yankin na Karamar Hukumar ta Tarauni, ranar Sabar din da ta gabata.

Haka zalika, Kawu ya bayyana matukar damuwarsa, bisa yadda ake samun yanayi irin na cudanya a tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwa, ta yadda za ka hangi namiji a tsakanin mata yana daukar hotuna, “wannan ko kadan ba tsari ne irin Addininmu na Musulunci ba.” Saboda haka, muka kuduri aniyar bujiro da sabbin tsare-tsare, musamman a wannan bangare domin tsaftace harkokin bukukuwanmu.

Wakilin al’ummar ta Tarauni a Majalisar Wakilan Nijeriya, ya cigaba da cewa, muna fatan nan ba da jimawa ba, za a daina ganin maza a tsakanin mata da sunan daukar hoto a ire-iren wadannan lokuta na bukukuwa. Ya kara da cewa, idan muka samu nasarar wannan shiri, mata ne za su cigaba da gudanar da wannan sana’a ta daukar hoto a lokacin shagulgulan da suka shafi mata zalla.

Haka kuma, ko da hoton Fasfot idan akwai mata a cikin sana’ar, sai dai kawai su shiga cikin gidaje domin daukar hoton ‘yan uwansu mata kadai, ba kamar yadda aka saba yi a baya ba.

“Mu na fatan idan wadannan mata guda 100 suka kammala samun wannan horo,  mun tsara ba su jari tare da kayan aikin da suka shafi na’urar daukar hoton da sauran kayayyakin da ke da alaka da sana’ar daukar hoton baki-daya.”

Har wa yau, yayin da ya ke gabatar da nasa jawabin a lokacin kaddamar da bayar da wannan horo ga wadannan Matasan ‘yan mata guda 100, jagoran APC  a Karamar Hukumar Tarauni, Alhaji Talle Mohammad Mai Unguwa, ya bukaci masu hannu da shuni da su yi koyi da irin wannan kyakkyawan tsari na wannan wakili, ya ce ko shakka babu, al’ummar Tarauni na alfahari da wannan bawan Allah, musamman ganin yadda ya rungumi kawo sabbin tsare-tsaren da za su kawo cigaban al’ummar wannan yanki baki-daya.

Talle ya kara da cewa, a lokacin wannan wakili ne, Shugabannin Jam’iyya tun daga kan matakin mazabu suka tabbatar da cewa, sun samu wakilin da ya san darajar al’umma tare da Shugaancin Jam’iyya. Sannan kuma, shi ne wakili daya tilo da ya samar da Ofis a kowace mazaba, ya kuma samar da babban Ofsihinsa wanda a koda-yaushe yake bude tare da samar da Ma’aikata wadanda ya dora wa alhakin sauraron duk wani mutun dan asalin wannan Karamar Hukuma da ya zo, domin gabatar da bukatun yankin da ya fito. Kuma Alhamdulillahi, duk lokacin da ya shigo Kano ya kan zauna a Ofis din, domin gana wa da al’ummar da yake wakilta.

Guda daga cikin matan da suka amfana da wannan horo kan sana’ar daukar hoton, Sumayya Umar, ta bayyana farin cikinsu bisa wannan tagomashi, inda ta ce wannan sana’a ce mai tarin albarka, musamman idan aka yi la’akari da yadda Allah Ya kawo lokutan da aka zamanantar da harkokin bukukuwanmu, wanda kuma abin takaici a lokacin gudanar da walima ko yinin biki, maza ke shiga cikin mata suna daukar hoto, wanda ko kadan wannan bai dace da tsarin al’ada da kuma Addininmu ba.

Saboda haka, sai Sumayya ta gode wa wakilin nasu a Majalisar Wakilai ta Tarayya bisa wannna abin alhairi, wanda ta yi alkawarin yin amfani da abinda a ka koya mu su domin gudanar da harkokin sana’ar ta daukar hoto.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: