Connect with us

RA'AYINMU

Dawowar Kasafin Kudi Daga Janairu Zuwa Disamba

Published

on

Bayan jerin ayyuka takuru, majilisar dokoki da kuma majalisar zartarwa ta gwamnatin tarayya sun samu nasarar kawo karshen bayanan kasafin kudade na shekara biyu tun lokacin da a ka kowa mulkin dimokradiyya a shekarar 1999.

Bayan mika kasafin kudaden shekarar 2020 a watan Disamba da ta gabatar, an matsa da bayanan kasafin kudade tun daga watan Janairu zuwa Disamba. Kasafin kudaden ya samu tsaiko sakamakon matsin tattalin arziki da kasar take fama da shi. Babu shakka kasafin kudi yana taka muhimmiyar rawa ga tattalin arziki da kuma tsare-tsaren cigaban.

Muhimman ababan more rayuwa su ne ke kara sa tattalin arziki ya bunkasa. Sakamakon muhimmancin da kasafin kudi ya ke ga cigaban kowacce kasa, kasashen duniya su na daukar lokaci wajen tsara kalandar kasafin kudi. Duk tsarin da a ka bi dai, dole a cikin kalandar kasafin kudi sai an samu lokacin fara gudanar da kasafin kudi da kuma lokacin kammalawa. Muhimmancin tsara kalandar kasafin kudin dai yana da yawa wadanda su ka hada da tabbatar da horo domin a samu ingantaccen tsari.

Kasafin kudi shi ne, matsayin injin da gwamnati take bi wajen neman bunkasa tattalin arzikinta na wannan shekara. Samun tsaiko wajen gabatar da kasafin kudi yana janyo a samu matsaloli wajen gudanar da harkokin gwamnati na wannan shekara, haka kuma za a samu tsaiko wajen masu zuba hannun jari na cikin gida wadanda suke amfana lokacin da gwamtani ta aiwatar da ayyukanta, saboda kasuwancinsu yana tsayawa cik sakamakon rashin aiwatar da kasafin kudi na wannan shekara.

Saboda ba a sami lokacin aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati ba, sakamakon tsaiko da aka samu wajen gudanar da kasafin kudi na wannan shekara.

A cikin kasafin kudin na shekara mai zuwa an kara kudaden harajin kayayyaki daga kashi biyar zuwa 7.5, wato kari tun daga Naira tiriliyon 8.83 na kasafin kudin shekarar 2019 da kuma kasafin kudin shekarar 2018 na Naira tiriliyon 9.12.

Mun tabbatar da cewa, sabon tsarin zai dauki tsawon lokaci kafin a fara aiwatar da shi, duk da irin kudaden da a ka samu da wanda a ka ci bashi domin a inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, amma ana samun tsaiko wajen gudanar da kasafin kudin.

Muna yaba wa shuwagabannin majalisar dattawa wajen gano matsalolin da a ke samu ga tsohon tsarin da ake bi wanda ke kawo cin hanci da rashawa da rashin duba makarraban gwamnati da na ‘yan kwangila, wanda ya hana kasar nan ci gaba. Mun tabbatar da cewa, da wannan sabon tsarin na wannan shekara, za a samu lokacin aiwatar da kasafin kudade musamma ma wajen gudanar da tattalin arzikin kasa yadda ya kamata da kuma kudaden da gwamnati tarayya take tunanin za ta kasha.

Aiwatar da kasafin kudin shekarar 2020 da wuri, zai fitar da ‘yan Nijeriya daga cikin matsin tattalin arziki a wannan shekara. Kalandar bayanai kasafin kudi a Nijeriya yana farawa ne tun daga watan Junanru zuwa watan Disamba, idan aka kwatanta da wasu shekarun, kafin wannan shekara, gwamnatin Nijeriya ba ta taba gudanar da kasafin kudi kan lokaci ba kamar na wannan shekarar, shi ya sa ake samun tsaiko wajen gudanar da harkokin gwamnati. A wasu lokutan, ‘yan kasuwa masu zaman kansu na kasa su kan samu matsaloli masu yawa wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu sakamakon rashin aiwatar da kasafin kudi da wuri har zuwa wata uku ko kuma wata hudu.

Kamar yadda ake da watanni 12 wajen gudanar da kasafin kudi, ya kamata gwamnati ta samar da wani bangare wadanda za su dunga aiwatar da lamarin cikin sauri. Yin hakan shi zai sa a dunga aiwatar da kasafin kudin cikin gaggawa. Aiwatar da kasafin kudi cikin gaggawa yana taimaka wa harkokin gwamnati. Tun lokacin da a ka koma mulkin dimokradiyya a shekarar 1999 ake samun matsaloli wajen gudanar da kasafin kudi wanda ke haifar da rashin ci gaban wannan kasa.

Wannan sabon tsarin da aka samu na kasafin kudi zai sa kasar nan ta samu sauki wajen gudanar da ayyukanta da kuma tsare-tsarenta.

Muna tabbatar da cewa, bayanan kasafin kudade tun daga watan Junairu zuwa Disamba, zai kawo ci gaba ga dukkan bangaren tattalin arzikin wannan kasa, sakamakon yin watsi da tsarin da ke kawo tsaiko wajen gudanar da kasafin kudaden.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: