Connect with us

RAHOTANNI

Islamiyya Ta Yi Walimar Haddar Kur’anin Dalibanta 27

Published

on

Ranar Lahadin da ta gabata makarantar Nurul Faila Lil Tahfizul Kur’an Kareem Wadirasatil Islamiyya, wadda ke Unguwar Juma a birnin Zariya, ta yi walimar kammala haddar Alkur’ani mai girma na daliban makarantar guda 27.

Tun farko a jawabinsa, shugaban makarantar Malam Ibrahim Bayi ya bayyana cewar sun kafa makarntar ce shekara biyu da suka gabata inda suka fara da dalibai Maza da mata dari hudu, wanda a halin yanzu kamar yadda ya CE, su na dalibai fiye da dubu biyu da suke karatu a makarantar, a bangaren karantun Alkur’ani mai girma, musamman Haddar Alkur’ani.

Ya ci gaba da cewar,daliban da suka kammala makarantar wasu da dama su na ci gaba da karatu a makaranru gaba da sakandare da kuma Jami’o’i, musamman Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da sauran Jami’o’i da su ke ciki da wajen Nijeriya.

A game da matsalolin da su ke addabar makarantar kuwa, Malam Ibrahim Bayi ya ce, tun kafa makarantar a zaurukan al’umma su ke koyar da daliban da su ke Yaye wa.

A kan haka ne Malam Ibrahim ya yi kira ga al’umma da su kawo was wannan makarantar tallafi da zai iya zama silar samun waje na su na din – din – dim, domin su Sami damar ci gaba da koyar da daliban da suke wannan makarantar.

Shi ko Garkuwa ayyukan Zazzau, Injiniya Ibrahim Balarabe Musa, nuna matukar damuwarsa ya Yi na yadsa mafiya yawan daliban da suka kammala haddar Alkur’ani Mai girma da kuma sauka, dalibai mata ne a kan gaba.

A Nan ne Garkuwa ayyukan Zazzau Injiniya Ibrahim Balarabe ya ce lokacin ya yi da iyayen yara za su fadaka, a cewarsa, bai dace ace iyayen yara mata Hafizai su aurar da ‘ya’yansu ga na mijin da ba shi da ilimin addini ba,said ya ce a nan gaba babu wanda zai nemo aure a Zariya, said an yi bincike a kan matsayin ilimin addininsa.

A dai lokacin wannan walima, shugaban kwamitin makarantar Shekh Sani shawartar iyayen yara ya Yi na su kara SA ido ga ilimin yaransu Maza, musamman a wannan lokacin da mata ke gaba a duk wani walimar sauka ko haddar Alkur’ani mai girma a wurare da dama, ba karamar hukumar Zariya kawai ba..

Sauran wadanda su ka Yi jawabi a wajen walimar, sun hada da kansila Mai wakiltar gundumar Unguwar Fatika a karamar hukumar Zariya, Alhaji Yusha’u Mohammed,inda ya yaba wa mahukumta da kuma  malaman makarantar, na yadda subka jajirce, wajen koyar da dalibai karatun addinin musulmi , musamman Alkur’ani mai girma, ya na shirye ya ci gaba wannan makaranta gudunmuwa,domin su sami damar aiwatar da ayyukan da suka SA wa gaba, na inganta rayuwar matasa, Maza da mata.

A karahen taron walimar, Mahaddata 27 da suka kammala haddar Alkur’ani Mai girma,sun karbi shahadar kammala wannan makaranta da kuma kyaututtuka daga shugabanni makarantar.

Wannan walima ya Sami halartar shugaban kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya Dokta A.A.Ladan da Dokta Ibrahim Umar Ibrahim,Limamin masallacin Albabello da kuma fitattun malaman addinin musulcin daga ciki da wajen jihar Kaduna.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: