Connect with us

RAHOTANNI

Sarauta: Maso Dan Adalan Gombe Sun Kwankwansa Kofa A Fadar Gombe

Published

on

Zuriyar gidan Mabani sun kwankwasa kofa na nemawar wa Muhammad Baba Mabani, Maso Dan Adalan Gombe a Masarautar Gombe domin zama daya daga cikin mashawartar Sarki.

Gidan Mabani, sanannen gida ne a Bundu wailaru dake Tudun Wada a cikin kwaryar Gombe wanda kuma kowa yasan Mahaifin su mutum ne mai daraja da kamala wanda ‘Ya’yan sa ma sun gaji wannan hali.

Da ya ke godiya a fadar Mai Martaba a madadin yan uwa a lokacin da suka je kwankwasa kofar Yayan Muhammad, din Alhaji Gidado Muhammad Mabani, yace sun taho ne kwai da kwarkwatar zuriyar gidan Mabani da yan uwa da abokan arziki suka zo fadar mai martaba Sarkin  na Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III dan rokarwa dan uwan su wannan sarauta ta Maso Dan Adalan Gombe.

Gidado Mabani, ya kara da cewa gidan Bubayero gida ne mai tarihi kuma gida ne dake karbar kowa a matsayin dan gida shi yasa suka taho da kokon su na bara dan neman wannan sarauta saboda ganin cancantar sa amma idan Sarki yaga wannan sarauta ta Maso dan Adala, ba ta dace da shi ba duk wacce a ka ba su su na godiya.

Ya kuma ce kudi ko isa bai sa Sarki ya bai wa mutum Sarauta sai ya ga dama shi yasa suka yo gangami su ka zo roko kansu a kasa a gaban sarki dan mika kokon baran na su.

Gidado Mabani ya ce, shi Muhammad Baba, yana da dattaku kuma in Allah ya yarda za’a same shi da rikon amana wanda ba zai yarda ya dinga fadin sirrin fada a ko’ina ba domin jama’ar gari ma sun shaida irin kamalarsa.

Muhammad Baba, yana aiki tare da kowa ba banbanci addini bare na kabilanci hakan ne ma tasa yan kabilar Igbo da Yarbawa musulmai da kiristoci suka shiga tawaga aka rako shi fada dan kwankwasa kofar neman wannan sarauta.

A cewar sa Muhammad mutum ne mai taimakon al’umma kuma an shaide shi bai da girman kai saboda komai kankantar mutum yana mu’amula ta kwarai da shi.

Da ya ke  maida jawabi a madadin Mai Martaba Sarkin Gombe Yeriman Gombe Hakimin cikin gari Alhaji Abdulkadir Abubakar, ya bayyana musu cewa tunda sun zo sun kwankwasa kofa su jira Sarki baya gaggawa wajen yanke hukunci ida ya duba ya yi nazari zai shawarci yan majalisar sa sannan za’a sanar da su yadda aka yi.

Yeriman Gombe, ya kuma ce kar dan an ba shi Sarauta ya zama mai yayata sirrin masarauta a wajen mutane ta kowacce hanya ya zama mai rike sirri kar dan sarki ya nemi shi sun yi shawari ya dauka yana gayawa mutane ba’a haka.

Daga nan sai ya tabbatar musu da cewa suje idan mai Martaba ya gama nazari za su ga dan aika ko ita sarautar da suka nema din ko wata daban da Sarki yaga yafi dacewa da’a ba shi.

Shi dai Muhammad Baba Mabani, Ma’aikacin gwamnati ne wanda kuma shi ne babban Akanta na kungiyoyin hada kai na ma’aikatun gwamnati wato CFA Co-operatibe and Financing Agency Gombe.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: