Connect with us

RAHOTANNI

Yadda BASEPA Ta Yi Gwanjon Buhun Gawayi 600 Da Ta Cafke

Published

on

Hukumar Tsaftace Muhalli ta Jihar Bauchi (BASEPA) ta yi gwanjon buhunan gawayi har guda 600 da ta cafke daga hannun masu sare dazuka da safaran Gawayi barkatai a jihar.

Wakilinmu ya shaido mana cewar hukumar ta saida kowani buhun gawayin ne a kan kudi naira 800 ga masu so, inda aka yi kiyasin sun tara kudaden da su kai naira dubu 480,000 da suka ce za su shigar da su cikin lalitar gwamnatin jihar.

Wakilinmu ya shaido mana cewar farashin dukkanin Gawayin da hukumar ta saida zai iya kaiwa kusan miliyan daya a kasuwa, domin kuwa wasu wuraren suna saida buhun Gawayi a naira dubu 1,500 wasu kusan dubu 2,000.

Da ya ke bayani wa manema labaru a lokacin gwanjon gawayin a karshen mako, babban sakataren ma’aikatar muhalli ta jihar Bauchi, Ahmad Muhammad Zalanga, ya shaida cewar sun yi kamen ne a ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata a karamar hukumar Dass, inda kuma suka sake yin wani wawan kamun a ranar 22 ga watan Oktoban da ta gabata a kauyen Zaranda da ke karamar hukumar Toro,

Ahmad Muhammad Zalanga, ya shaida cewar sun yi samamen ne domin dakile aiyukan masu lalata dazuka da sare itatuwa barkatai a jihar, don haka ne ya bayyana cewar gwamnatin jihar ba za ta taba bari wasu marasa kishi na lalata dazukan jihar ba.

A cewar shi, akwai hatsari babba da ke barazana wa al’umma ta hanyar lalata dazuka, ya bayyana cewar kwararar Hamada matsala ce da ka iya jawo wa jiha ci baya, don haka ne ya nemi jama’a su basu hadin kai domin shawo kan matsalolin da suke akwai.

Ya ce, sun bi matakai na doka wajen saida Gawayin da suka cika hanyensu da su a lokacin da suka kai farmaki ga masu safaransu, “Doka ta ba mu dama kuma akwai amincewa daga kotun majistiri da ke kula da harkokin wannan ma’aikatar da cewa kayyakin da aka kama ya kamata a yi gwajensu a kudi mai rahusa kuma wa kananan mutane ba wai wadanda za su je su sayar ba. Mun sayar wa masu amfani da shi,”

“Mu babban fatanmu shine ma a daina amfani da Gawayin gaba daya kamar yadda aka ce a daina sare dajuka,” A cewar Zalanga.

Ya ce sun karya farashin Gawayin gami da saida wa talakawa, daga bisani kudaden da suka tara sun shigar da su cikin lalitar gwamnatin jihar domin yin amfani da su ta hanyoyin da suka dace domin hakan ya zama izina ga masu aikata laifukan.

Ya ce, kimanin buhun Gawayi dari shida 600 ne suka cafke gami da yin gwanjensu, “Dukkanin gawayin an kamesu ne a lokacin da jami’anmu suka kai samame yankunan, kuma za mu ci gaba da kai samame muddin masu sare itatuwa suka ki dainawa to muma ba za mu daina kamesu da ababen da suka saro ba,” A cewar Ahmad.

Babban sakataren ya ce, muddin masu sana’ar sare dazuka da sunan yin gawayi suka ki dainawa, to tabbas gwamnatin jihar za ta ci gaba da dandana musu kudarsu har sai sun bar lalata mata dazuka.

Ya kuma ce wadanda suka kame a bisa irin wannan sana’ar suna gurfanar da su a gaban kotunan da ke kula da hidimar, kana wasu kuma suna tura su kai tsaye ga jami’an ‘yan sanda.

Da ya ke karin haske kan halin da sha’anin ke ciki, Babban sakataren dindindin na ma’aikatar muhalli ta jihar, ya ce, “Muna son jama’a su kula sosai. Muna jin labaran abubuwan da suke faruwa a wasu wuraren, ga shi abubuwan da suke faruwa a wasu wuraren har sun fara tunkaro. Misali a nan jihar, muna da wurare bangare-bangare, duk wanda ya san arewacin Jihar Bauchi wadanda Allah bai wadatasu da manyan itatuwa ba sai kananan itatuwa a sakamakon yanayin kasar na sahara ya san irin illar da Saharan ake musu. Haka ma wai ba a hakura ba sai an sare kananan itatuwan da suka ragen, to ina ganin muna fuskantar matsala babba.

“Ya kamata mutane mu guje wa abun da zai zo ya daga hankali, kowa shaida ne a lokacin da aka samu wani guguwa da iska mai karfi yayi ta’adi sosai a jihar nan shekarar da ta wuce, sakamakon yadda wurarenmu suka zama babu itatuwa masu kare muhallai daga kwararon Hamada, babban matsala ce hakan, don haka muna kira ga jama’a da suke shuka itace da bishiyoyi domin amfaninsu
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: