Connect with us

KASASHEN WAJE

Yiwuwar Amurka Da Iran Su Sasanta Ta Kara Dusashewa

Published

on

Yiwuwar Amurka Da Iran Su Sasanta Ta Kara Dusashewa

Yiwuwar Iran da Amurka su sake bullo da wata sabuwa kuma tartibiyar yarjajjeniya kan makamin nukiliya ta dusashe ga dukkan alamu, a kalla a halin yanzu, bayan da shugabannin kasar Iran su ka fito kiri-kiri su ka yi shakulatin bangaro da yarjajjeniyar da aka cimma a 2015, wadda Shugaban Amurka Donald Trump ya janye daga ciki tun a 2018.

Zaman dardar dai na dada tsanani saboda akwai yiwuwar a kara kakaba ma kasar Iran takunkumin kasa da kasa baya ga wadanda tuni Amurka ta kakaba ma ta.

Shugaban Iran dai ya ce akwai yiwuwar tattaunawa da Amurka, to amma Shugaba Trump ba amintacce ba ne wajen batun tattaunawa da cin ma jituwa:

Shugaba Rouhani ya ce, Da ace akwai amintattun mutane da ke jagorantar Amurka, da abin ya zo da sauki. Yayin da aka ce daya bangaren ba amintacce ba ne, abubuwa kan zama da wuya.

Zuwa yanzu dai kasashen biyu sun kauce ma yaki kai tsaye tun bayan da Amurka ta kashe wani babban janar din sojin Iran.

A wani labarin kuma, Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi jagoran juyin-juya halin Iran Ayatollah Ali Khamenei kan kalamansa na jiya jumaa da ke zargin Washington da rura wuta kan kuskuren harbor jirgin Ukraine da Iran ta yi dama batun nukiliyar kasar baya ga sabbin takunkuman da Trump ya sake laftawa Tehran.

Cikin sakon Twitter da Trump ya wallafa ya gargadi Khamnei da ya kula da kalamansa, kan barazanar da ya ke kokarin yiwa Amurkan da nahiyar Turai dungurugum, yana mai cewa babban kuskurene yadda Khamene’i ya bayyana kasashen Faransa, Birtaniya da kuma Jamus a matsayin yan amshin shata ga Amurkan.

Cikin kalaman na Trump ya ce maimakon Khamnei ya tsaya tsara kalamai don muzanta kasashen kamata ya yi, yayi tunanin halin da tattalin arzikin kasarsa ke ciki da kuma rigingimun da ke gabanta baya ga halin matsin rayuwar da alummarsa ke ciki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: