Connect with us

MANYAN LABARAI

Gwamnan Bauchi Ga Tsohon Gwamna: Ka Zo Ka Taya Ni Gyara Barnarka

Published

on

Halastaccen Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulqadir Muhammad, ya miqa katin gayyata ga babban abokin hamayyarsa, wanda ya kayar a zaben 2019, wato dan takarar jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar, Muhammad Abubakar, da ya zo su hada hannu wuri guda, domin ciyar da gwamnati mai ci da jihar Bauchi gaba.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labarai da babban mai taimaka wa Gwamnan Jihar Bauchi kan hulda da ‘yan jarida, Muktar Gidado, ya rabar wa ‘yan jarida a Bauchi, ya bayyana cewar gwamnan jihar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Abuja bayan tabbatar ma sa da nasarar zabensa da Kotun Qoli ta yi jiya Litinin, 20 ga Janairu, 2020.

Gwamnan ya bayyana cewar hada qarfi da qarfe wuri gudan, zai baiwa gwamnatinsa zarafi da damar shawo kan dumbin matsalolin da jihar ke fuskanta da kuma tabbatar da kyautata jihar Bauchi zuwa ga mataki na gaba.

“Na miqa hannayena don mu yi musabaha da abokin hamayya na kuma dan takarar APC da na kayar, Muhammad Abubakar ne domin mu tabbatar da aiwatar a aiyukan da shi ya gaza yin su,” a cewarshi.

A kan hakan, Sanata Bala Muhammad ya bayar da tabbacin gwamnatinsa na tabbatar da shugabanci na kwarai da baiwa jama’an jihar tabbacin samun ababen more rayuwa a qarqashin jagorancinsa.

“Nasarata da hukuncin da kotu ta tabbatar min, yana qara tabbatar da inganci tsarin shari’a a qasar nan, ina son na tabbatar wa al’umman jihar Bauchi da suka amince suka zabeni, zan tabbatar da yin gwamnatina ba tare da nuna wariya ko banbanci ba,” A cewar halastaccen gwamnan jihar Bauchi da kotun koli ta tabbatar.

LEADERSHIP A YAU ta naqalto cewar a hukuncin da kotun kolin ta yanke a qarqashin Justice Dattijo Mohammed, kotun ta bayyana cewar zarge-zargen da APC da dan takararta, Muhammad Abubakar suke yi kan zaben gwamnan jihar Bauchi da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris din 2019 zarge-zarge ne marasa inganci, don haka ne ta bayyana cewar masu qarar sun kasa tabbatar da tuhume-tuhumensu don haka ne ta kori qarar bisa rashin sahihanci kana ta tabbatar da Sanata Bala Muhammad na jam’iyyar PDP a matsayin halastaccen gwamnan jihar Bauchi.

Kotun ta tabbatar da cewar qarar da jam’iyyar APC da dan takararta Muhammad Abubakar suke yi kan zaben gwamnan jihar Bauchi da ya kai ga baiwa Sanata Bala Muhammad na PDP nasara ya gaza samun inganci, don haka ne kotun ta yi watsi da qarar.

Kotun Koli ta ce, zaben da aka yi sahihi ne, an kuma bi dukkanin matakai na doka da oda wajen aiwatarwa, kana hukuncin da kotun zabuka da kotun daukaka qara suka yi, sun yi daidai kan zaben gwamnan jihar.

Yanzu haka dai Sanata Bala Muhammad shine ya samu zarafi da ikon kasancewa a gwamnan jihar, wanda zai shafe shekaru hudu cif yana jagorantar jihar Bauchi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: