Connect with us

RIGAR 'YANCI

Kotun Koli: Bukukuwan Murna Sun Barke A Kano Bayan Nasarar Ganduje

Published

on

A ranar Litinin ta jiya ne birnin Kano mai dimbin tarihi ya cika da murna da bukukuwa a sa’ilin da labarin samun nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya isa birnin a hukuncin da Kotun Koli ta zartar.

Wakilanmu sun lura da yadda milyoyin al’ummar jiharsu ka fito a cikin matsanancin sanyi, inda su ke taruwa a wurare daban-daban su na tattauna nasarar da Ganduje din ya samu tare da bayyana farin cikinsu.

Damuwar da ta cika birinin na Kano, kafin yanke hukuncin duk ta kau, inda mutane su ka fito ta ko’ina su na cigaba da harkokinsu ba tare da nuna wata damuwa ba kuma.

Da ya ke magana a kan nasarar ta Ganduje, Kwamishinan yada labarai da al’adu na Jihar, Malam Muhammad Garba, cewa ya yi hukuncin yin Allah ne da kuma tabbatar da abin da mutanen jihar su ka zaba.

A cewarsa: “Mu na nuna matukar godiyarmu ga Allah mai girma da daukaka a kan wannan nasara da ya bamu. Wannan nasarar ba ta Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ne ba kadai, nasara ce ta al’ummar Jihar Kano.

“Mu na kira ga mutanan Jam’iyyar PDP da su tabbatar sun zauna lafiya, su kuma karbi wannan hukuncin da kyakkyawar fata. Wannan nasarar kuma tana kara tabbatar da mafarin tafiyarmu ce zuwa mataki na gaba.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: