Connect with us

LABARAI

Nijeriya Za Ta Tallafawa Kasar Guinea Gina Matatar Man Fetur

Published

on

Hukumar Kula da Ci Gaba da Sa Ido wato ‘Nigerian Content Development and Monitoring Board (NCDMB)’ ta ce za ta hada kai da kamfanin Waltersmith Petroleum Oil Limited domin taimaka wa kasar Equatorial Guinea wurin gina kananan matatun man fetur.

Babban Sakatare a ma’aikatar, Simbi Wabote ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da majalisar gudanarwar hukumar ta fitar a Abuja ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce ya yi wannnan bayanin ne a lokacin da ya karbi bakuncin ministan ma’adanai na Equatorial Guinea, Mista Gabriel Lima a harabar karamar matatar fetur mai tace ganga 5,000 a kullum da ake ginawa a Ibigwe na jihar Imo.

Ya kara da cewa gina matatun na Equatorial Guinea zai bai wa Najeriya damar fitar da nata man sannan ta kara yawan ma’adanan da ake samarwa daga hydrocarbon.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: