Connect with us

DAGA NA GABA

Hon. Sabo Musa: Gwarzonmu Na Mako (3)

Published

on

Cigaba daga makon jiya.

 

Me ya ja hankalinka ka fara siyasa

To, ni dai tun tashi na ina jin ba dai-dai ba ne a ce sojoji ke mulkarmu. Tun ba ni da wayo ina jin zafin hakan. Saboda haka ana fara siyasa don kagarar da na yi sai na shiga  GNPP da aka kafa,tunda ita ce farko. Ba zan manta ba na samo takardunta na zo gida malam Yakuku yake cewa “ to kai siyasa za ka yi amma ka shiga GNPP ka bari su malam Aminu Kano za su kafa tamu ta Kano sai ka shiga” Tun lokacin abin ya dau hankalina. Na zo na shiga NPN har aiki na yi  karamarar hukumar Gwaram a 1983 na yi sakatare na matasa.

 

Waye ubangidanka?

Ba ni da wani ubangida sai dai a lokacin da mu ka fara jam’iyyar NPN na fada miki garin mu daya da Alhaji Bello Maitama, wato Gwaram, kuma yana da karfi a jam’iyyar, sannan a na yin jam’iyyar a garin, in ana taro ina zuwa har ina yin magana. Da suka lura Ina da hikima ta magana sai suka fara kirana. Lokacin Sabo Bakin Zuwo yana PRP, sai suka rika kira na da Sabo Bakin zuwo na NPN. A  wannan lokaci na yi sha’awar siyasa kwarai da gaske.

 

To me ya sa suka ja ka haka a jiki?

To! ni ban sani ba amma dai ina ganin har da rashin tsoro in ina magana wanda wannan kuma ina iya tuna wa akwai lokacin da malam Aminu Kano ya shigo Gwaram lokacin Shagari yana shugaban kasa,  akwai wata makarantar Awwakawa a  ciki ana lacca, lokacin da  Sule Lamido yana jawabinsa yana sukar Shagari kai tsaye ba tsoro bayan ya soki Bello Maitaman ya ce ba za su yi  magana da shi ba  su suna magana ne da mai hula birki kunne ( wato  an siffanta yadda Shagari yake sa hula) da shi suke. Wannan magana ita ta kara zaburar da ni na sa a zuciyata nima in zan yi magana zan ke yin zafi ne. Don haka ina matashin duk da kankantata duk inda zan yi magana ta manya ne sai ya zamana ma in an je taro har ana kagara a ba ni na yi magana. Kin kuma san siyasa tana son iya Magana. Kuma har yanzu haka ne ko lokacin da malam Aminu Bello Masari ya fito takarar gwamna ni na yi MC ga duk wasu wakilai da suka zo ni nake fara yi musu bayani sannan shi  ya yi nasa bayanin. Da aka tafi kamfen 2015 ni nay i MC duk wanda za a gabatar a kan diro ya yi Magana ni na gabatar da shi kuma duk wanda zan kira nasan abin da zan fada wanda zai bayar da sha’awa shi kuma ya ba shi karkashi haka su ma mutane za su ji karsashin son ya hau din don su ji me zai ce.  Saboda duk wanda yake siyasa Katsina na sanshi in har ya isa ya hau diro. A kowacce jam’iyya kuwa yake,  haka duk wadanda suka rike mukamai da wadanda ke jam’iyya da wadanda suka shigo. Duk  kananan hukumomi kaf da muka je talatin da hudu Allah ya taimake ni ban fadi wata Magana da za ta haifar da rashin fahimta ko ta haifar da fitina ba ko a ce Kash! Me ya sa aka ce haka. Haka ma 2019 ni na yi.

 

Me Yasa ka bar PDP duk da gudummawar da ka ba ta?

To Gaskiya ni siyasa ta mutum nake ba na ba wa jam’iyya karfi. Ina PDP lokacin da aka gama zaben malam Umaru Musa, wannan gwamnan na yanzu yana majalisa tare muke ko da yaushe. Lokacin da PDP ta tsayar da Obasanjo sai na ce ban kuma yin PDP ni ba na sonsa. Sai kuma ANPP ta tsayar da Olu Falae sai na ga duk ba na yi don duk ban gamsu da su ba. Ana nan sai kuma Buhari ya yarda zai yi takara bayan an jawo hankalinsa. Allah ya jikan Kanti sai  ya sa aka kira ni ya ce “to ga aikin da muka dauko ku ba mu goyon baya mu tunkare shi har sai ya zo ya yi siyasa”. Rana guda muka je muka shiga jam’iyya ni da Buhari. Ko wannan APC din da aka ganni a ciki saboda shi Masari ne da Buhari su kadai. Ba don Buhari na takara ba Masari na takara nan PDP na zauna. Saboda ‘yan PDP na saba da su ina tare da su amma kuma ga wasu da nake so su shugabance ni su kuma suna APC don haka na dawo APC.

 

Ya alakarka da ‘yan PDP din da ka baro?

Ba wanda nake da matsala da shi. Kin ga kusa da Shema nake kuma duk abin da dan’adam key i wa mutum Shema yay i min ban taba bacinsa  ba haka kuma dukkan shugabannan ban bata da kowa ba. Don haka duk abin da ya faru gidana  yadda za ki ga ‘yan jam’iyyar APC haka za ki ga dan PDP ya zo. Tunda nake siyasa ina Magana a radiyo sama da shekara talatin ina Magana a manyan kafafen yada labarai kamar BBC da sauraansu , ina hawa diro ina shiga kafafen yada labarai na cikin gida, amma ban taba zagin wani ba akan siyasa. Ban taba wulakanta wani ba sai dai na iya maganganu nan a yarfa jam’iyya mutane su tsaneta amma mutum da mutuntakarsa in bata shi ko in wulakanta shi a shekarun nan da na yi ina siyasa ban taba yi wa wani ba. Kuma ko an yi min ba zan taba ramawa ba.

 

A ganinka wanne kokari ka ke alfahari da shi wanda ku ke ganin ya taimaka wajen karya gwamnatin baya?

Akwai wani shiri da muka yi a 2015  wanda muke ganin yana daga cikin yunkurinmu ya karya PDP  2015.Mun yi shi ne  a gidan radiyon bishan mai suna Masari Ja mu je! Kullum muna daukar batu na wani abun da PDP ta yi wanda ya kamata mutane su sani  sai mu yi Magana a kai. Wani na yi, wani lokacin na samo wanda zai yi sai da muka kwana arba’in muna yi kullum. Ban taba yin kwata ba. Kin ga kawai daga Allah ne. Kuma da wannan shirinmuka kai PDP kasa.

 

Ga ka Malamin Addini ga ka dan siyasa ya kake hada abubuwa biyu mabambanta?

Ni ban taba hada addini da komai ba. Lokacin da Masari ya ba ni mukami sai da na fada masa ni fa in ana aikin izala to fa ba na yin komai sai wannan aikin. Don haka ko yanzun nan aka ce muna da wa’azi to fa kome ne ne a gabana zan bar shi ne nan take  ni zan tafi. Kuma Alhamdlillah mai girma gwamna ya fahimce ni bai taba cewa a’a ba. Ba alfahari ba ko jiya makarantun islamiyya uku na je na saukar karatu. Kuma ni ban ma taba gajiya ba ina ma jin dadin duk wani abin addini a kira ni. Kin ga ina cikin shuwagabannin kungiyar izala ta Katsina a matsayin iyaye tunda muna rike da shugabanci a matakin kasa. A matsayina na Darakta protocol ko a ina za a yi wa’azin ko da a wajen kasar nan ne kamar Nijar ko Ghana duk ina cin masu shiryawa. Gaskiya ina ba wa addini muhimmanci, saboda shi ne rayuwata. Don ina kallon kasuwancina da ma siyasar wani abu ne dan kankani na rayuwar duniya. Duk da Allah bai hana nema ba to amma kuma kada neman duniya ya shagaltar da kai.

 

To a Matsayinka na Dan siyasa kuma ga ka da Wani Bangare na Addini ya Tafiyar ta ke?

Ni duk abin da ya shafi addini ba na wasa da shi, kin ga ai izala nake  ai kasancewata a bangaren izala duk abin da ya taso na darika ina yinsa iya karfi na. Misali akwai lokacin da makarantar Sheikh Dahiru Bauchi take da wata matsala ta fili a kusa da makarantarsu suke so su mallake shi wajen shekara goma don fadada makarantar ni na shige gaba na yi ma gwamna  Magana,  gwamna ya sa na nemi  mai filin  shi kuma mai filin y ace ba zai sayar ba gwamna ya ce a fada masa ko wanne irin fili yake so a Katsina za a ba shi.  Mun  muka je muka yi jagoranci aka saye shi miliyan goma sha. Ni kowa na wane ba don siyasa ba, saboda Allah. Kuma bari ki ji,  duk litattafan da izala suke amfani da su shi,  da su darika take amfani. Duk littafin da izala ta yarda da su malaman darika ta yarda da shi. Tun daga kawa’idi da ahalari da ishmawi da risala da iziyya da Bukhari da Turmuzi da Ibn Maja duk wadannan littattafai su darika ke amfani da su kuma su izala ke amfani da shi. Don me kuma malamai ke rarraba kan mabiya? don me ba za su ji tsoron Allah su hada kai ba? Izalar nan tun ranar da aka kafata da mu aka kafata randa aka zo aka fara tunanin a yi wa’azi da mu a wajen, duk inda za a je ina matashi yaro karami da ni za a je. Saboda shi Sheikh Yakubu Musa su suka kafata. Wa’azin farko da ni aka yi na biyu da ni aka yi. Duk inda aka yi gwagwarmaya aka nemi kashe ‘yan izala irin su Abakalake da Wudil da wasu wurare ina ciki. Ba na mantawa mun je Wudil wa’azi mutanen Wudil kowa da itace. Kwamishinan ‘yan sanda na Kano da  ’yan sandansa, DPOs dinsa na kusa duka sun tare Wudil ba za mu yi wa’azi ba. Haka aka bugi na buga.

 

A siyasa daga lokacin da ka fara ci gaba aka samu ko ci baya?

To! An ci gaba a wani bangaren sannan an ci baya a wasu wuraren. Misali da idan kuna jam’iyya duk wanda ke jam’iyyar kana sonsa sannan ana mutuntaka duk kankantarka ko dai kai talaka ne ko kankanta na shekaru ba a wulakantaka. Duk wani abu da ya taso na jam’iyya za a yi da kai. Amma yanzu abin ba haka ba ne. Misali yanzu jam’iyyar APC nake kuma tun da aka kafata ba a fi wata hudu ba na shige ta amma tunda na shiga shugabannin da ke rike da jam’iyyar APC ba su aminta da ni ba. Ba su sona ba su hulda da ni rana daya ba su taba hulda da ni.

 

Kuma ka ci gaba da zama a  cikin jam’iyyar?

To ai wadannan mutanen Buhari da Masari don su nake yi sannan idan ma na bi ta kansu ashe soyayyata ba ta cika ba.  Don haka  da wuya ki yi sati daya ba ki ji ni a radiyo ko jarida ba ko warta kafar sadarwa ina kare gwamnatin APC. Kin ga nasan siyasar da Akwai lokacin da na yi wasu maganganu aka zabi Obasanjo shugaban kasa na taba gidan Katsina da Daura. Wannan ya harzuka masarauta aka zo ofishina aka farfasa yarana da ke wajen aka buge su aka yi min kaca-kaca da ofisa. Kan wannan kes din da muke yi a hedikwatar ‘yansanda sai da Buhari ya taso shi da mutanensa suka zo wajena a hedilkwatar saboda ina dan jam’iyya kin ga kishin jam’iyya irin na lokacin baya kenan.  Kuma ina cikinta kuma ina da bakin kare ina yi mata hidima amma su ba ma za su iya kareta ba. Nima ma kuma ina cikinta ne saboda Buhari da Masari yau in har ba sa ciki nima ba zan zauna ba. Akwai lokacin ina NPN a Gwaram a shekarar 1982  sai wasu ‘yan PRP suka tare ni da daddare a lokacin ba wayar hannu amma ba a yi minti talatin ba an zo wajen ana fada saboda kare mutumci na.

 

Akwai Masari Restrotion awareness forum  da ka ke shugabanta a jahar Katsina me ne manufarta?

Lokacin da gwamna Masari ya ci zabe  ya shekara biyu yana ayyuka amma mutane ba su san me ake yi ba saboda ya fi bayar da karfi akan harkar ilimi. Wanda alkawari ne ya yi tun wajen neman zabe kan zai ba harkar ilimi muhimmanci saboda muhimmancin ilimi. Don haka yana hawa sai ya dauko ward  361 na jahar Katsina a kowanne ward a ciki ya dauki makarantar da ta fi lalacewa a duk ward din, a wasu ward din ma makarantu biyu wasu uku a wasu ma har makarantu hudu ya sa aka gyara wadannan makarantu.

Kawai  sai ‘yan adawa suka fara shiga radiyo suna cewa gwamnatin fenti kuma  kowa ya na ji amma an yi shuru. Ba ma a makarantu ya tsaya ba har da asibitocinmu na Katsina da na Daura  da Funtua da Dutsinma duk an farke su ana ta gyaransu. Wasu ma suna cewa maimakon wannan abi da ake yi a gina wani mana. Sai muka ga mu wajibin mu ne mu wayar da kan mutane kan haka misali na asibitocin  ba su san yanzu in kana son ka gina asibiti irin na Katsian  General Hospital ba sai kin tafi kila sai kin wuce Shinkafi sannan ki sami wurin da za ki yi. Idan hanyar Jibia ne sai kin wuce barikin Soja sannan ki sami fili ko ma wajen Tsanni. Kuma idan aka gina sabon asibiti aka bar wannan duk wadanda suke takawa da kafa a cikin gari saboda ba shi da abin hawa ko babu kudin abin hawan kin ga ba zai je asibitin ba.

Wannan tausayin al’ummar ya sa gwamnati ta ce wannan da muke da su a bare shi a mayar da su na zamani. Asibitocin nan duk na tsofffin kananan hukumomin a yanzu ko asibitin Abuja bai gwada mana komai. Ganin wannan sai na kira al’umma na ce ku zo mu kafa Restoration domin mu wayar da kan mutane mu fada musu mai Masari yake yi. Muka rin ka zuwa ziyara mu dauko hoto sai mu zo mu gwadawa al’umma. Haka Mukai ta yi sai muka yi ta buga littatafai mun buga su da yawa wadanda sun shafi ayyukan.

Mun fara da kanann littatafai har manya. Muka rika yin banoni muna aikawa kananan hukumomi sananan muka rinka fadi a radiyo a talabijinma muka sami wani fili muka sa masa Kyawun alkawari cikawa yau shekara uku muna shirin  duk litinin abin da gwamnati ta yi muke fadi har yanzu ba mu gama ba.

 

Au ku ka yi tunanin hukumar ma kenan?

Eh mu muka kafa abarmu . Gwamnati tana can da aikinta mu kuma nan muna namu a haka muka zagaye kanann hukumominmu 34 muka gano ayyukan da aka yi muka fadawa ‘yan Katsina daga sannan kowa ya yi shuru. Ta haka muke tallata manufofin nasarar.

 

Kwanan nan an ganka kana rabon kayan sanyi ga Almajirai sannan kana kiran kowa ya fito ya  yi me ya janyo ?

A tarihina da na ba ki na fada miki na yi almajiranci, ba bu mai ba mu wajen kwana ko riga babu mai ba mu takalmi babu mai ba mu abinci babu mai babu mai kai mu asibiti in ba mu da lafiya  ko abin rufa. To fa lokacinma mutane da ma tausayi  ba kamar yazu ba. Ina yawo na ga yaro a sanyin nan yana bakin baranda yana rawar dari na tambayi daga wanne gari yake ya ce min bai san garinsu ya sunan babanka y ace bai sani ba. Wannan shi ne dalili da ya sanya na ga yaran nan ba su da laifi in ma da laifi wadanda suka kawo su su ne da laifi. Don haka na yi kira ga al’umma sannan na sa masu rubutu na restoration su rubuta ku roki masu arziki da jami’an gwamnati da masu arzkin unguwa su taimakawa almajiran unguwarsu. Muna cikin dakunanmu da riguna mun kunshe da mu da ‘ya’yanmu amma yaran nan suna nan bakin titi da baranda ba tabarma ga sauro ga ba mayafi. Bayan mun yi kira sai muka taimaka mu ma da abin da Allah ya hore mana. Dalibin kur’aini ya fi karfin wulakanci.

 

Kana cikin ‘yan gaba-gaba a kaunar Buhari sai kuma ga shi babbar sana’ar da ka ke alfahari da ita ita ce sayar da mota ga kuma doka kanta ba ka ji soyayyar ta ragu ba?

To ai doka ce ta kasa kuma kasar ta yarda ko da ban ji dadi ba ai ba abin da zan yi doka ce. An ce kowa ya yi duty gashi nan muna yi shikenan. Duk da yadda ake cikinkin kafin a yi wannan dokar yanzu ba a yi amma ai komai Allah ne ya kaddara duk abin da Allah bai kaddara ba ba mai iya yinsa mu kuma mun yi Imani da kaddara duk wadda ta zo.

 

Menene ka ke kallo ya zama silar nasararka a rayuwa

Nasarata daga Allah take sannan akwai iyaye. Na yi hakuri na zauna da mahaifana lafiya. Kullum suna shi min albarka , kullum da safe in gari ya waye in je na debo ruwa a daji na cika randuna na gidanmu in ci dumame sannan na dau jaki na zuba taki na kai gona in da damuna ne in mun yi noma mun tashi in yi ciyawa in kawo wadda za a ba wa dabbobin gidanmu. In na dawo sai na kuma dauko ruwa na kara cika randa. Haka na zauna na yi biyayya kullum yana shi min albarka har Allah ya yi masa rasuwa. Ko lokacin da na dawo Katsina na sami wuri, ita ma mahaifiyata sai na dawo da ita kusa da ni a cikin gidana ta rasu. Ina son mahaifiyata tana sona lokacin da za ta rasu tana ciwo mai zafi in an zo wajenta ba ta ko motsi amma sai aka rika kokwayon magana ta da an yi sai a ga tana yunkuri, mun rabu da ita lafiya. Manzon Allah ( S.A.W) ya ce addu’ar uwa ko uba akan da kamar addu’ar manzo ne akan al’umma tai. Kin ga amsassa ce. To tsakani da Allah mun rabu  lafiya. Kin ga ban yi boko mai zurfi ba kuma karatun addinin ma ban yi zurfi ba amma duk abin da ake a Najeriya ina iya yinsa duk wanda ake magana da shi a Najeriya ina iya yi ba na shakka. Don haka nasarata daga Allah ne. Kuma Alhamdlillah na godewa Allah.

 

Me ne Burinka?

Burina na cika da Imani duk wata ni’ima Allah ya yi min. Ina zaune lafiya da matana 4 da ‘ya’ya talatin da hudu da jikokina goma sha biyu. Da gidana da wajen sana’ata. Ina da rike da mukami a gwamnati.

 

Ba ka da niyyar takara kenan a 2023?

Ba ni da niyyar takara ba ma wanda zai kuma ba ni mukami na amsa alhamdillah na gode wa Allah.

 

Ko da Allah ya ba wa Masarin wata dama a gaba?

Ina son Masari na yarda da shi in ya ce zo ka yi min masinja zan yi masa saboda ina sonsa na yarda da shi mutumin kirki ne. Shi yasa ki ka ga wannan wahalar da nike sha a jam’iyyar na hakura na zauna saboda shi. Amma ina fatan na ci gaba da aiwatar da sana’ata har karshen rayuwata ba abin da ba zan yi ba. Ni ya fi min.

 

Wanne kira gareka gun matasa musamman na jahar Katsina kan dogaro da kai

Kullum in ka bude radiyo kira ake wa’azi ake yi ‘yan siyasa kuma kullum kira suke yi kan matasa . Matasa ya kamata ku yi wa kanku fada . Yanzu kalli gwamnatin Katsina haka kawai ta dauki matasa mutum dubu biyar duk watan duniya tana ba su albashi don su tattala su yi jari su yi sana’a amma kasha 95%  ba sa yin sana’ar da an ba su sai su kashe. Wannan kudin suna iya yin jari kuma ya kai su inda ba su taba tsammani ba. Misali ko ni kaina da na fara sayar da mota ba ni da taya ina karbar ta mutane ne na sayar, yanzu bana karbar motar kowa duk motocin da ki ka gani ciki da waje duk nawa ne. Kada ki manta wanda ya fi kowa kudi a Afrika Dangote ne an ce mahaifiyarsa ta ba shi naira dubu dari da ita ya fara dubi inda ya kai shi a yau.

Idan yau Dangote zai je wannan gari ya je wannan neman na abinci, kai wanene? An ba ka dubu ishirin an ba ka dubu goma duk  wata amma ka ki tattali  kuma a jima ka dorawa Allah kana rokon wani. Wannan dubu ishirin in dai ka karba da kyakkyawar zuciya kamar yadda duk wata Masarin ya ba su da kyakkyawar niyya don kada su zame wa al’umma matsala ya kamata su ma matasa su yi ma kansu fada  ai a baya na fadi yadda na ke yin ciyawa ko tono kasa da kananan sana’oi don dogaro da kai ni ban ma taba rokon wani ba. Alhali mahaifiyata na nan amma na kudurce a raina sai dai ni na nema na ba ta. Dubi yau ba ga shi ya zama alheri ba.

Matakan da gwamnati ta dauka na tallafawa matasan nan shi ne dai-dai. Abin da mutane ba su sani ba ita gwamnati tana da tsari yau in gwamnati ta karbo giran dinta ta ba wa al’ummarta don ta tallafa musu ya yi daidai kamar yadda gwamnatin tarayya ta yin power da dpower haka ko a Libiya gwamnatin Gaddafi ta yi. To kira na ga matasa da al’umma su kalli abin da kyakkyawar niyya. Ba na mantawa akwai lokacin da Masari ya dawo daga tafiya ya kira mu ya ce daga nan har bodar Katsina mu duba mu ga yaran da suke da sha’awar sana’a sun dan kasa wani abun na sayarwa  mu dauko duk sunayensu.

Haka mu ka je muka yo lis muka kawo.  Ya ce to dukkansu kowanne mu ba shi dari da hamsin- hamsin. Haka muka yi fadin jahar nan har sau biyar. Nan craft billage matasa ake koya ma aiki kuma duk wanda aka koyawa nan take za a ba ka kayan aikin sannan a dauki kudi a baka a ce ka je ka kama shago kada ma ka ce babu kudin kama shago. Haka aka yi wa masu sana’ar sayar da abinci sai an ba ka komai kamar firiza da gas da kula da duk abin da za a bukata masu kiwon kaji kafinta.

Banda wannan akwai BATC duk irin gadon da za asaya a Dubai suna iya yinsa ga gyaran injin mota da ma bangare na injin motar suna iya yinsa a wajen haka na Daura daga ko’ina a Arewa ana zuwa. Hatta mata ma suna yi. Duk inda kuma aka yi wadannan har da mata ba a warewa.

 

Wanne kira za ka yi wa Al’ummar kan taimakon juna su san hakkin na kan kowa

Jama’a ya kamata dai su sani abin da ka taimaki al’umma shi za ka iske a lahira amma wanda ka ci kai kadai ka ci.

 

Mu na godiya kwarai.

Ni ma na gode sosai.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: