Connect with us

LABARAI

Kungiyar Fataken Shanu Na Zargin Miyatti Allah Da Yi Ma Ta Makarkashiya

Published

on

Kungiyar Fataken Shanu da ke kai shanu sassan Nijeriya daban-daban ta na zargin kungiyar Miyatti Allah da yi ma ta zagon kasa wajen gudanar da sana’arsu.

Shugaban kungiyar na Jihar Zamfara kuma ma’ajin kungiyar na kasa, Alhaji Aminu Garba Gasau, ne ya bayyana haka a lokacin da ya kira taron ‘yan jarida a Tsohuwar Kara da ke Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.

Alhaji Aminu Garba Gusau ya bayyana cewa, “mun kammala lodin shanu, domin tafiya kudancin kasar nan, kamar yadda mu ka saba, sai ga shi wasu sun kawo masu rasiti daga ofishin Miyatti Allah na jihar cewa, dole su yanki wannan rasitin. Idan kuwa ba su yanka ba, duk inda su ka je da shanun a wajen jihar, jami’an tsaro za su kama su a matsayin shanun sata.”

Shugaban kungiyar ya kara da cewa, “ganin zuwan rasitin Miyatti Allah, wanda ba mu san daga inda ya samo asali ba, mu ka fahimci makircin da a ke son kulla ma na, idan mutanenmu sun bar wajen jihar.

“Don haka mu ka ga ya dace da mu kira ku, ’yan jarida, mu sanar da ku halin da mu ke ciki, don a watan da ya gabata an kama ma na tirela biyu a kudanci kasar nan; wai da sunan shanun sata. Kungiyarmu ta je, su ka bincika, su ka tabbatar ba na sata ba ne.

“Kuma babu wanda ya aika koken an sace ma sa shanu daga Zamfara. Duk da haka sai da mu ka samu asara na mutuwar shanu takwas. Wannan dalilin ne  ya sanya mu ka kira ku, domin ku bayyana wa duniya halin da mu ke ciki.”

Shugaban ya bayyana wa ‘yan jarida shaidun takardarsu a kungiyace da sa hannun shugaban sojoji na mai kula da shiyyar Sokoto da kuma takarda daga ofishon sufeto janar na ‘yan sanda na tabbatar da su a matsayin kungiyar Fataken Shanu.

“Kuma a nan Gusau mu na bin ka’idojin daukar shanu da tantace su daga wakilan jami’an tsaro na masu kula da lafiya dabbobi kuma mu na biyan kudin haraji a koyaushe. Kuma mu na da hotunan da wadanda su ka sayar ma na dabobi tare da dabbobin, don kauce wa sayen shanun sata,” in ji shi.

Alhaji Aminu Garba ya kuma tabbatar da cewa, kungiyarsu ita ce wacce ta kai wa Gwamna Bello Matawalen Maradun ziyara kuma ya amshe su a matsayin shugabanin kungiyar, amma sai ga wasu daga baya su na neman raba kungiyar biyu.

“Su ka kira mitin a ofishin Miyatti Allah na jihar Zamfara su ka yi mitin dinsu ba tare da mu ba; wai mu rika ba wa kungiyar Miyatti Allah kudin rasiti duk lokacin da mu ka yi lodi. Idan kuwa ba haka ba, shanunmu na sata ne.

“A kan haka mu ke kira ga gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagoranci Gwamna Bello Matawalen Maradun a kan ta shiga tsakanin masu neman kawo ma na tarnaki wajen harkar kasuwancinsu, kuma mu na tabbatar wa gwamnatin jihar Zamfara mu ma mu na goyon bayanta a kan kokarinta na samar da tsaro da kuma kawo hadin kan al’ummar jihar ta Zamfara. Ba mu tare da masu neman raba kan al’ummar jihar Zamfara,” a cewar shugaban.

Sai dai kuma, a taron da a ka yi a ofishin Miyati Allah na Jihar Zamfara, shugabanta na Jiha, Alhaji Tukur Jangebe, ya bayyana cewa, fidda rasitin masu lodin shanu sun yi shi ne a matsayin hadin gwiwa da shugabannin kungiyar Fataken Shanun da Sarakunan Zango, dan kauce wa sayen shanun sata.

Shi ma Kwamishinan Tsaro na jihar Zamfara, Hon. Abubakar Dauran, ya tabbatar da goyan bayan gwamnatin a kan rasitin kuma ya bayyana cewa, kungiyar Fataken Shanu daya ce; ba ta rabu biyu ba. Wato ita ce wacce Surajo Sani Abuga ke wa jagoranci.

Wani, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa wakilinmu cewa, “ya kamata gwamnati jihar ta shiga cikin wannan rikici, don ta kawo karshenshi, domin da karfin tsiya a na neman raba mu biyu, alhali guda mu ke. Idan ba so a ke a lalata ma na harkar kasuwancinmu ba.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: