Connect with us

LABARAI

Kwana Biyu Kafin Zabe Dan Takarar APC Da Magoya Bayansa 10,000 Sun Koma PDP A Sakkwato

Published

on

Dan Takarar Majalisar Dokoki na Jihar Sakkwato a zaben raba gardama da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa, Hon. Bature Muhammad Binji ya canza sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP da magoya bayansa 10, 000 tare da jaye takararsa a jiya.

Dan Takarar ya canza sheka ne kwana biyu kacal kafin zaben raba gardama da Hukumar Zabe za ta gudanar a Mazabar Dan Majalisar Dokoki da ke Wakiltar Karamar Hukumar Binji. Za a gudanar da zaben ne a dalilin bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba ta hanyar soke zabe a rumfuna hudu da kotun sauraren karar zabe da kotun daukaka kara suka yi bayan zaben 2019.

Hakan ya nuna cewar dan takarar PDP, Hon. Umar Sahabi wanda ya fara jan zaren wakilci a zaben 2019 zai ci karensa babu babbaka ba tare da wata hamayya ba a zaben wanda Hukumar Zabe za ta gudanar a yankin wanda yake na PDP ne.

Hon. Bature Binji wanda shine Dan Majalisar Binji a 2015 zuwa 2019 ya bayyana cewar ya canza sheka ne da magoya bayansa 10, 000 saboda gamsuwa da salon mulki da siyasar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal wanda ya bayyana a matsayin shugaba mai gaskiya, adalci da cika alkawali.

“An gudanar da zaben farko, Tambuwal ya samu nasara, an sake na biyu, ya yi nasara, mun je kotu har sau uku duka yana samun nasara a kan mu. Shin ya za a yi ka ci-gaba da jayayya da ikon Allah? Don haka na jaye takara ta na kuma zama manba a PDP da magoya baya na dubu 10, 000 kuma za mu bayar da goyon bayan mu ga dan takarar mu na PDP a zaben da za a gudanar.” Ya bayyana.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jiha, Ibrahim Milgoma wanda ya karbi tsohon dan takarar a Hedikwatar Jam’iyyar ya bayyana canja shekar Hon. Bature Binji zuwa PDP a matsayin nasara ga jam’iyyar da kuma koma-baya ga APC musamman ganin cewar a yanzu za a gudanar da zabe babu hamayya. Ya ce da tsofaffi da sababbin manbobin PDP duka matsayinsu daya kuma za su ci-gaba da yi masu adalcin da suka saba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: