Connect with us

KASASHEN WAJE

Girgizar Kasa Ta Hallaka Mutum 21 A Gabashin Turkiyya

Published

on

Akalla mutum 21 suka mutu, sama da mutum dubu kuma suka samu raunuka sakamakon wata girgizar kasa mai karfi a gabashin Turkiyya.

Girgizar kasar mai girman 6.8 ta faru ne a garin Sivrice da ke lardin Elazig inda girgizar kasar ta yi sanadiyar rushewar gine-gine da kuma tursasawa jama’a da dama garari kan tituna.

Rahotanni sun bayyana cewa an ji motsi ko kuma karamar girgizar kasa a Syria da Lebanon da kuma Iran da ke makwabtaka da kasar.

Tuni dama an saba samun girgizar kasa a Turkiyya inda a shekarar 1999 mutum 17,000 suka mutu a wata girgizar kasa mai karfi da ta faru a garin Izmit da ke yammacin kasar.

Girgizar kasar da ta faru a Turkiyya a ranar Juma’a ta faru ne da misalin karfe 17:55 agogon GMT.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: