Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim din ‘Kar Ki Manta Da Ni’

Published

on

Suna: Kar Ki Manta Da Ni.
Tsara labari: Ali Nuhu .
Kamfani: FKD Film Productions.
Shiryawa: Naziru Dan Hajiya.
Bada Umarni: Ali Nuhu.
Sharhi: Musa Ishak Muhammad.
Jarumai: Ali Nuhu, Shamsu Dan Iya, Umar M Sharif, Rabi’u Rikadawa, Saratu Gidado, Maryam Booth, Maryuda Yusuf da sauransu.
Fim din Kar Ki Manta Da Ni, fim ne da a ka gina shi a kan labarin wani masoyi mai suna Nasir (Shamsu Dan Iya), wanda ya tsinci kansa a wani mugun yanayi na shaye-shaye, a sakamakon masoyiyarsa da ya rasa wato Ummi (Maryam Booth). Shi dai Naseer da Ummi sun dauki dogon lokaci su na soyayya, sai dai soyayyar tasu ta gamu da matsala sakamakon umarni da mahaifin Ummi ya bawa Nasir, a kan ya fito ya aure ta idan har da gaske ya na son aurenta. Sai dai a wannan lokacin Nasir ba shi da karfin da zai yi auren, shi kuma mahaifinta ya matsa a kan cewa lallai sai ya aurar da ita.
Wannan dalili ne ya sa a ka aurar da Ummi ga wani dan attajirai wato Isma’il (Umar M. Sharif). Tun daga wannan lokaci ne Nasir ya samu kansa cikin mawiyacin hali, wanda ya jefa shi cikin matsanancin shaye-shaye, wanda hakan ya tilasta masa kora daga aiki saboda sata da ya fara yi domin samun kudin shaye-shaye. A haka dai Nasir ya yi ta rayuwa a birkice, saboda ba shi da wani wanda zai tamaka masa ya ja a jiki, saboda daman ya rasa mahaifiyarsa a gidansu.
Rayuwar Nasir ta fara dawowa dai-dai ne a lokacin da kawunsu (Ali Nuhu) ya zo gida ya same shi a cikin wannan mawiyacin hali, wanda hakan ya sa a ka dauke Nasir a boye a ka maida shi gidansa. A gidan ya ci-gaba da samun kulawa, domin har likitan kwakwalwa a ka kawo masa domin ya ci-gaba da kula da shi.
Bayan Nasir ya warware ne, sai kawunsa ya maida shi makaranta domin ya ci-gaba da karatu. A nan ne kuma su ka kara haduwa da Ummi ita ma an kawo ta makarantar. Da farko ya ki kula ta, amma daga baya ta ja hankalinsa, har ya zauna ya saurari labarinta cewa ai ta fito daga gidan mijinta sakamakon matsaloli da su ka yi ta samu. A karshe dai Nasir da Ummi sun sake dawowa fagen sabuwar soyayya.
ABUBUWAN YABAWA
1. Fim din ya samu aiki mai kyau.
2. Sunan fim din ya dace da labarin fim din.
3. Hotuna sun dauku, kuma sun tsaru.
4. Babu matsalar sauti a fim din.
5. An nuna tasirin soyayya ta gaskiya.
KURAKURAI
1. Ginin labarin a farkon fitowar fim din bai tsaru ba kamar yadda ya kamata, domin akwai rudarwa kadan ga masu kallo.
2. Ta ya ya Abdul ya san iyayen Ummi, har su ka amince da shi domin ya taimake ta?
3. Babu sunayen jarumai, ma’aikata, da Kuma shi kansa fim din, a farko ko karshensa, kamar yadda kowanne fim ya saba zuwa da shi.
4. Sanya rubutun harshen Faransanci bai da alaka ta kusa da fim din.
kARkAREWA
Duk da matsaloli kadan da fim din Kar Ki Manta Da Ni ya samu, abubuwan yabawansa sun zarce matsalolin. Fim din ya yi nasara sosai, musamman wajen rike masu kallo tun daga farko har karshe. Fatanmu dai shi ne, samun karuwar nasarori ga wannan masana’anta ta fina-finan Hausa wato Kannywood.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: