Connect with us

KANNYWOOD

Ya Kamata Mata Su Rungumi Sana’ar Dogaro Da Kai- Habeeba Sanda Lemu

Published

on

Leadership A Yau Lahadi ya tattauna da matashiya wadda ta rungumi karatun boko da sana’a lokaci daya, da ta bari kokarin neman ilimin boko ya hada ta rungumar sana’ar rufa wa kanta asiriba, lallai wannan wani darasi ne ya kamata matasa su runuma a wannna loaci. Matashiyar mai suna Habeeba Sanda Lemu ta bayyana wa Editanmu yadda ta fara sana’ar da irin kalubaken da ta fuskanta da kuma irin ribar da ta samu a harkar sana’ar. Ga dai yadda irar ta kasance.
Zamu So Ki Fada Wa Masu Karatumu Sunanki.
Sunana Habeeba Sanda Lemu, wanda aka fi sanina da sunarsSana’ar da nake yi, wato lakani na maitake ‘GLAMOUROUS’.
Menene Takaitacen Tarihin Ki?
Da farko dai an haife ni ne a garin Minna, babbar birnin jihar Neja a ranar Asabar 12 ga watan Fabrairu, na halacci makarantar FOMWAN Islamic school dake Minna, bayan na kammala matakin farko na karatun Firamari da Sakandari, natafi zuwa makarantar Senior Secondary a Challenge International School duk dai a garin na Minna, bayan na kammala na samu kyakyawan sakamako mai kyau sai na cigaba da karatun mataki na uku wato karatun jami’a, a Ibrahim Badamasi Babangida University Lapai, dake nan jihar Neja ina kuma karatun ne a fannin jarida (Mass Communication).
Ta Yaya Kika Fara Wanann Sana’ar Ta Yi Wa Mata Kwaliya?
Na fara koyan kwaliya ne tun ina karama, tun kafin insan zai zama sana’ar hannu na, saboda ina sha’awar yin kwalliya sosai, na zauna a gaban madubi na tsawon loakci yayin makeup, hat na kware daga nan ne na yi shawarar mayar das hi sana’ata, tun ina yi mutane gida har nba fara yi wa makwabta daga nan wasu suka fara zuwa daga nesa, har kuma suna nay a shawara da sana’ar gaba daya.
A Halin Yanzu Kin Kai Shekara Nawa Kina Wannna Sna’ar Na Yi Wa Mata Kwalliya?
Lallai zuwa yanzu na kai misalign shekara 5 zuwa 6, kamar yadda na fada da farko, na fara koyon sana’ar ne a kan kanne na yanzu gashi alhamdullilahi na kware kwarai da gaske.
Ko Zaki Bayyana Wa Masu Karatunmu Irin Nasarorin Da Kika Samu A Yayin Gudanar Da Wannan Sana’ar?
Alhamdulillah, cikin nasarorin dana samu ta hanyar wannan sana’ar suna da daman gaske, amma baban nasara shhi ne na yi mutane da dama kwalliya kuma an yaba a sosai. Kwaliyar kuja sun hada dana bikin aure da suna da na murnar zagayowar ranar haihuwa wato Birthday da sauransu, kuma na samu abinm sanya a aljihu, na taimaka wa iyaye na daidaigwargwado.
Kowanne Sana’a Nada Matsaloli Da Akan Fuskanta Yayin gudanar Da shi, Wadanne Irin kalubale Kika Fuskanta A Yayin Gudanar Da Wannan Sana’ar?
Lallai na na fuskanci kalube da dama, wasu mutane za su zo suyi kwaliya suce ma za su turo da kudin kikin ta account sai kaji shiru, wasu kuwa za su bada rabi su roke ka Allah da Annabi za su ciko daga baya amma sai kayi wahala kafin ka amsa, wani sa’in kayi ta buga waya ba a dauka, wasu ma in kagama aikin sai kawai su ce jeka ka dawo amma ba wai suna da nufin biyan kudaden bane. Haka kuma na kan fuskanci kalubale, yayin da nike fuskantar jarabawa ko kuma wani abu mai mahimmanci sai kawai wasu fu nemi a zo a yi masu kwalliya da dai sauran matsaloli
Me Babban Burin Ki A Kan Wannan Sana’ar?
‘Babban buri na shi ne wannan sana’ar tawa ta bunkasa sosai, a kara sanina a kan sana’ar a fadin karamar hykumarmu da jiharmu dama nijeriya baki daya, ina kuma da burin koyawa matasa ‘yan uwa na wannan sana’ar don suma su samu abin dogaro da kai da kuma kare mutuncinsu.
Ko Kina Da Wani Shawara Ga ‘Yan Uwan Ki Matasa?
Shawara ta ga matasa yan uwana shi ne su tashi tsaye su koyi sana’ar hannu koman kankantarsa kada su raina sana’a, matukar za ta rufa musu asiri, ta haka za su samu cikakken mutunci a tsakanin abokansu, za kuma su samu na tallafa wa iyayensu da ‘yan uwansu.
Daga karshe Ko Kina Da Shawara Ga Gwamnati Kan Tallafa Wa Matasa Masu kokarin Riko Da Sana’a?
Shawarata ga gwamnati shi ne su taimaka wajen tallafa wa al’umma musamman matasa don kara musu kwarin gwiwa ta hanyar gina masana’antu don horar da matasa aikin dogara da kai, haka kuma ya kamata gwamnati ta samar da hanyoyin bashin kiudade daga bankuna ga matasa don su kara inganta sana’o’insu.
Malama Mun Gode Kwarai Da Gaske
Ni ma na Gode
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: