Connect with us

NOMA

Dalilin Hukumar NiMet Na Gargadar Manoma

Published

on

Hukumar has hashen yanayi  NiMet ta shawarci manoma su guji sauri ko yin gaggawar shuka amfanin gona a farkon faduwar ruwan saman kakar noman bana.

Ta sanar da hakan ne a cikin bayani da rahoton da ta fitar a Abuja inda ya bayyana cewa ta sanar da hakan ne gudun kada ruwan ya dauke zuwa wani lokaci har karancin ruwan ya sa su tafka asara.

Ta sanar da cewa, bayan farkon zubar ruwan shuka a farkon damina, za a fuskanci kwanaki kamar 10 zuwa 21 kafin ruwan ruwan sama ya sake zuba a jihohin Neja, Bauchi, Jigawa, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Kebbi, Yobe da kuma Barno.

Ta kuma sanar da cewa, hukumar zai faru tsakanin cikin watan Mayu zuwa cikin Yuni, inda kuma ta bayyana cewa a fara hasashen samun damina a yankunan Kudu Maso Kudu, tun a ranar 24 Ga Fabrairu.

Sannan rahoton ya ci gaba da cewa jihohi irin su Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina, Jigawa da Barno, su yi tsammanin faduwar ruwan shuka daga ranar 2 Ga Mayu.

A fara tunanin shigowar karshen damina tun daga ranar 26 Ga Satumba a Katsina da wasu sassa na Arewacin Sokoto, yayin da a yankin Neja-Delta kuma sai daga ranar 28 Ga Disamba za a fara ganin alamun karshen damina.

Tsawon lokacin damina a cikin 2020 zai kai kwanaki 110 zuwa 160 a wasu yankunan sahel na Arewa, yayin da a Kudu kuwa zai kai kwanaki 210 zuwa 280.

Hukumar ta NiMet ta ce za a samu ruwan sama daidai-da-daidai, sannan kuma za a fuskanci lokacin da ruwan saman zai yi yawa fiye da yadda ake bukata.

Hukumar ta ce za a samu yawan ruwan sama a Arewa wanda ya kai yawan gejin ma’auni 400mm, inda ta kara da cewa, a Kudu kuma yawan sa zai iya kaiwa gejin ma’auni har 3000.

Har ila yau, wannan rahoton ya nuna cewa za a iya samun yanayin da ruwan sama zai fara daga farko, daga nan kuma zai dauke zuwa wasu kwanaki masu yawa, kafin daga baya kuma daminar ta sauka ka-in-da-na’in.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: