Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gidauniyar Aliko Dangoe Ta Tallafa Wa Mata 34,000 A Katsina

Published

on

Gidauniyar Aliko Dangote ta tallafawa mata dubu talatin da hudu a fadin jihar Katsina da naira dubu goma kowace matae domin bunkasa kananan sana’o’in da zasu dogara da kansu.

Wannan shiri na da nufin taimakawa mata masu karamin karfi da suke da kananan sana’I’o ta hanyar karafafa masu gwiwa, inda aka zabi mace dubu a kawace karamar hukuma 34 da ake da su a jihar Katsina

Da yake jawabi a wajan bikin kaddamar da wannan shiri a karamar hukumar Batagarawa da ke jihar Katsina shugaban gidauniyar Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa gidauniyar tasa tana da nufin kashe makudan kudadan a Najeriya

Ya kara da cewa kimanin naira miliyan dubu goma aka ware domin tallafawa mata masu kananan sana’o’I a kananan hukumomi 774 da ake da su a fadin tarayyar Najeriya.

Alhaji Aliko Dangote ya ce wannan kari ne bisa kokarinsa na bayar da tallafi ga masu karamin karfi miliyan 300  a yankin arewa masu yamma a lokacin wata azumin Ramadan domin kara samun sauki rayuwa.

Ya yi kira ga wadanda suka amfana da wannan  tallafi da suyi amfani da shi  ta hanyar da ya kamata domin baiwa wasu dama nan gaba suma su amfana da irin wannan tallafi daga gidauniyar ta sa.

Da ya ke nasa ta’alikin, gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa naira dubu goma da za a baiwa kowace mace za su taimaka mata wajan bunkasa harkokin da ta yi na yau da kullin.

Ya kara da cewa wannan tallafi ya yi daidai da kokarin gwamnatinsa na bunkasa harkokin mata da a ka gudunar a bangarori daban-daban a fadin jihar Katsina ta hanyar wasu shirye-shirye da gwamnati ta bullo da su.

Gwamna Aminu Bello Masari ya nuna jin dadinsa da wannan tallafa da ya fito daga gidauniyar Aliko Dangote wanda yace ba karamin taimakwa zata yi ba ga mata masu karamin karfi a fadin jihar  Katsina.

Tun da farko da take nata jawabin shugabar kwamitin wannan shiri, Hajiya Rayyanatu Lawal wanda kuma ita ce babar Satakariya a ma’aikatar kasa da sufiyo ta bayyana hanyoyin da suka bi wajan zabar mutanen da za su amfana da wannan talaffi na gidauniyar Aliko Dangote

Hajiya Rayyanatu ta bayyana cewa wannan shirin yana a matsayin kaddamarwa ne, saboda haka za su shirya yadda za su cigaba da raba wannan tallafi a sauran kananan hukumomin 33 da su ka rage a fadin jihar Katsina.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: