Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Neja Ta sha Alwashin Samun Ingantaccen Lantarki Don Bunkasa Kasuwanci

Published

on

Gwamnatin Neja ta bayyana kudirinta na samar da ingantaccen wutar lantarki da tsaro, don bai wa masu sha’awar shigowa dan zuba jari da bunkasa kananan sana’o’i damar cin moriyar arzikin da ke jihar.

Kwamishina a ma’aikatar kasuwanci a jihar, Hon. Mustapha Jibrin Alheri ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan kasuwanci da hadaddiyar kungiyar ‘yan Kasuwa (CIPE)  da kungiyar masu sana’o’in hannu (NICOPA) ta shirya a Minna, a dakin taro na hotel din haske na yini daya.

Mustapha Alheri ya cigaba da cewar bisa kokarin mai girma gwamna, Alhaji Abubakar Sani Bello akwai yarjejeniya tsakanin gwamnati da hukumar da ke rarraba wutan lantarki hanyar da za a bunkasa karfin wutan lantarki ta yadda masu kananan sana’o’i da manyan kamfunna zasu anfani, wanda tuni mataimaki gwamnan jiha, Alhaji Ahmed Muhammed Ketso yayi nisa da tattaunawar.

Daga cikin muradun gwamnatin nan, shi ne bunkasa sana’o’i ta yadda jama’a za su samu ayyukan yi.

Ire-iren wadannan tarukkan abu ne mai kyau da zai nunawa gwamnati haske akan inda ta dosa, a shekarar 2018 NICOPA ta rubuto wa gwamnati shawarwari a kan hanyoyin da ya kamata a bi wajen bunkasa kasuwanci wanda akan shi mu ke yanzu, gwamnatin jiha ta mayar da hankali akan magance matsalar wutan lantarki, tsaro da gyaran hanyoyin jihar wanda suka kunshi sanya ido kan ganin an kammala aikin hanyar Suleja zuwa Minna, da Lambata zuwa Bida wanda mallakin gwamnatin tarayya ne. Yanzu haka a cikin wannan shekarar za a fara aikin hanyar Minna zuwa Bida wanda mallakin jiha ne, wadannan manufofin kudurce-kudurcen ne na gwamnatin jiha na ganin an inganta kananan sana’o’i a jihar.

Shugaban taron, Alhaji Abdullahi Sulaiman (Baban Inna) ya nemi hukumar kula da raba wutan lantarki da su lalubo hanyar da za a rika samun ingantaccen wutan lantarki wanda zai taimaka wajen bunkasar harkokin kasuwanci a jihar. Matsalar bunkasar arzikin kasa bai tsaya kan gwamnati kadai ba, hanya ce da kowa zai iya bada gudunmawa cigaban kasa, amma wajibi ne a tabbatar da ingantaccen tsaro da wutan lantarki.

Hon. Sa’idu Salisu ( Injaga) shi ne mataimakin shugaban karamar hukumar Chanchaga, yace akwai bukatar ‘yan kasuwa su shigo karamar hukumar dan kafa masana’antu, domin karamar hukumar Chanchaga a shirye take wajen baiwa ‘tan kasuwa hadin kai wajen bunkasa harkokin kasuwanci dan samar wa jama’a gurabun aiki da kuma karin samun kudaden shiga a jihar.

Desmond Rabo, wanda ya jagoranci shirya taron hadin guiwar daga cibiyar CIPE yace manufar shirya taron shi ne lalubo hanyoyin da za a bi wajen bunkasa harkokin kasuwanci a jihar Neja. CIPE da NICOPA mun fahimci ‘yan kasuwa na neman gudunmawar gwamnati wajen bunkasa harkokin tsaro da samar da kyakkyawar yanayi a jihar nan, sanin kowa ne jihar Neja kusan kowa ya dogara ga gwamnati ne, shi muka da cewar irin yadda jihar ke kunshe da tattalin arziki mai anfani idan aka yi hadin guiwa tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa za a taimakawa gwamnati wajen samun kudaden shiga sannan masu hannu da shuni zasu iya shigowa dan bunkasa kasuwanci a jihar ta yadda dubban jama’a zasu iya samun madogarar rayuwa.

Saboda haka idan gwamnati za ta yi anfani da dubarun mu, ta aiwatar da su yadda ya kamata za a samu damar bunkasar kananan kasuwanci kuma ita kanta za ta iya fadada hanyoyin samun kudin da ta, amma hakan ba zai yiwu ba dole sai an samar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a matakin farko, sannan a samar da ingantaccen wutan lantarki, da kuma hanyoyi wadannan sune matakan farko da ya kama bi, domin kusan shi ne muradin da muke son cin mawa a wannan tafiyar.

Masana da dama dai sun koka akan yadda rashin biyan kudin wutan lantarki daga jama’ar gari yake kokarin taimakawa wajen durkusar da hukumar bada wutan lantarki ta kasa.

Masanan sun bayyana bisa rahotannin da ke firowa daga hukumar rarraba wutan lantarki kusan kashi sittin da biyar masu anfani da wutan basa biyan kudaden wutan lantarki da suka anfana da shi, wanda ba karamin koma baya ba ne kuma ba zai haifar da da mai ido ba ga cigaban kasar nan ba kamar yadda ake bukata ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: