Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Kasar Sin Na Da Niyyar Cimma Nasarar Yaki Da Cutar Numfashi

Published

on

Ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya taron manema labaru a yau Lahadin, inda ya jaddada cewa, a karkashin jagorancin tawagar bada jagoranci kan ayyukan yaki da cutar numfashi a sanadin kwayar cutar coronavirus ta kwamitin kolin jam’iyyar JKS ta kasar, za a mayar da aikin yin rigakafi da shawo kan cutar a matsayin wani aiki a gaban kome, a yi iyakacin kokarin gudanar da aikin yadda ya kamata. A ranar 25 ga wata, ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar JKS ya kira taro, inda aka tsaida kudurin kafa tawagar bada jagoranci kan aikin tinkarar cutar, da tura tawagogin bada shawara zuwa yankunan da suka fi fama da cutar, ciki har da lardin Hubei da dai sauransu. Wannan ya nuna cewa, an mayar da aikin yin rigakafi da shawo kan cutar a matsayin koli, hakan ya nuna aniyar jam’iyyar dake rike da mulkin kasar Sin ta kiyaye tsaron jama’a da kiwon lafiyarsu, da kuma yadda take sauke nauyin dake bisa wuyanta na kiyaye lafiyar jama’ar duniya baki daya, lamarin da kuma ya shaida ingancin tsarin kasar.

A yayin da take fuskantar wannan yanayin annobar cutar da ta bulla a birnin Wuhan na lardin Hubei, kasar Sin ta dauki matakai masu dacewa cikin sauri, wadda ta samu tabbaci daga wajen kasashen duniya. A cikin ‘yan kwanakin da suka wuce, kafofin watsa labaru masu yawa a duniya sun mai da hankali kan sanarwar da birnin Wuhan ya bayar na kafa wani asibitin wucin gadi cikin kwanaki 6. Kafar watsa labarai ta BBC ta kasar Burtaniya ta bada sharhi mai taken “Me yasa kasar Sin zata iya kafa wani asibiti a cikin kwanaki 6”, inda ta bayyana cewa, “Saboda gwamnatin kasar Sin tana iya kawar da kowace irin matsalar da ake fuskanta sakamakon tsare-tsaren gwamnati, tare da hada karfi da karfe.”

Yanzu dai, akwai larduna da jihohi guda 30 na kasar Sin da suka kaddamar da matakan da suka kai matsayin koli da nufin tinkarar cuta mai tsanani da ta bulla ba zato ba tsamani, wanda ya shafi mutane sama da biliyan 1.3. Kana yankuna masu yawa na kasar sun turo kungiyoyin masu aikin jinya zuwa lardin Hubei, yanzu haka Sinawa biliyan 1.4 na kara hada kansu don yaki da wannan cutar numfashi. (Mai fassara: Bilkisu)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: