Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Katsina City News: Yadda Malam Danjuma Ya Bar Kyakkyawan Tarihi

Published

on

Sau tari mutum kan assasa abu wani ya yi nasara wani kuma a sami akasin haka musamman idan ya kasance ko dai ba a yi shi da kyakkyawar niyya ba ko kuma ba a sami hadin kan wadanda aka yi abin domin amfaninsu ba. A ranar 11-ga watan Fabarairun 2015 ne Malam Danjuma Katsina ya samar da wani dandali a whatsup wanda ya kira da Katsina City News. Manufar dai dandalin shi ne sanin mai jahar Katsina take ciki, sannan kuma wanne ci gaba take kai , in kuma an sani ci baya mai ne dalili sannan ina mafita take?

Dandalin ana zaune lami lafiya duk kuwa da ya tara duk wani rikuni na al’umma. Cikin dandalin akwai sarakai iyayen al’umma, ga duk wanda ya amsa sunansa a siyasa a Katsina tun daga lamba dayan jahar da mataimakinsa har zuwa kasa in dai dan siyasa na iya fita cikin al’ummarsa ya yi abin kwarai to yana nan a wannan zauren. Malamai magada Annabawa masu ijtihadi suna nan su ma ciki suna saita al’umma duk inda aka kauce su dawo da mambobi hanya. In kuwa ana batun attajiran jahar nan ne kat! Sanana akwai matasa da ‘yan jarida daga kowanne bangare wato talabijin da radiyo da jarida. Ma’aikatan gwamnati a wannan kafa suna da ‘yancin Magana. Duk wadannan mutane su na zaune masu mabambantan ra’ayi na akida da na siyasa sun yarda su zauna tare don ciyar da jahar Katsina.

A ranar 21-1-2019 wannan dandali ya shirya gagarumin taro don karrama wadanda suka samu mukamai a gwamnatin jahar Katsina a ma’aikatu kama daga kwamishinoni da sauran ofisoshi da aka nada da kuma ‘yan siyasar da su ka sami nasarar kujerar sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da majalisar jaha.

Gwamnan Jahar Rt Honourable Aminu Bello Masari shi ya bayar da ranar da za a yi taron kuma  ya lamunce a yi taron a gidan gwamnatin jahar. Abin Sha’awar duk wanda ya yi jinkirin zuwa taron, to tabbas maigirma gwamna ya riga shi halartar taron. Zuwan gwamnan wajen ya tabbatar da karamcin da aka shaidi gwamnan da shi tare da saukin kai da kasancewarsa mutum na mutane marar girman kai da iya mu’amala.

An fara taron karfe tara na dare khadi Alhafiz ya bude taron da addu’a  kamar yadda a ka tsara. Babban jojin jahar Justice Musa Danladi ya yi  Jawabin fatan alheri wanda yake dauke da nasiha mai ratsa jiki kan muhimmanci da hatsarin da yake tattare da kafofin zumunta a karshe ya yi wa haduwar fatan alheri. Danwairen Katsina Alhaji Sada Ruma ya yi jawabin maraba ga duk mahalarta taro tare da yi musu fatan alheri yadda suka zo lafiya Allah ya mayar da kowa lafiya.

Malamai masu wa’azi da fadakarwa sun hada da Malam Aminu Yammawa da Malam Saulawa. Bayan gama wa’azi da fadakarwa an gabatar da bada lambar girmamawar ga wadanda aka karrama. Wadanda aka karrama sun hada da:-

Maigirma Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari da mataimakin shi Ks. Mannir Yakubu da wasu ‘yan majalisar Tarayya da ‘yan majalisar jihar katsina da ‘yan majalisar zartarwa ta jihar Katsina da wasu masu rike da mukamai cikin Gwamnatin jihar Katsina aka karrama. An karrama   Alh Mutari Lawan da  Hon. Abubakar Yahya Kusada dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kankia, Kusada da Ingawa. Da Hon Sada Soli Jibiya dan majalisar Tarayya mai wakiltar Kaita/Jibi. Da Hon. Ahmad Dayyabu Safana dan majalisar tarayya mai wakiltar Dan musa, Safana, da Batsari. Da Hon. Musa Nuhu Gafiya dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Kaita. Da Hon. Ali Abubakar Albaba dan majalisar jaha mai wakiltar karamar hukumar Katsina.

Sauran sun hada da Hon. Rabe Nasir Kwamishinan ma’aikatar kula da ilmin kimiyya da fasaha ta jihar Katsina. Da Hon. Sani Aliyu Danlami Kwamishinan ma’aikatar harkokin wasanni da jin dadin jama’a. Da Alh. Idris Usman Tune shugaban ma’aikata na jihar Katsina (Head Of Serbice). Da Alh Babani Isah Mani (Durbin Katsina)  Da Hon. Ya’u Umar Gwajogwajo. Da Alh. Abdul Hadi Ahmad mai  taimakama Gwamna kan kafar sadarwar zamani (Social Media). Alh. Sabo Musa Hassan.  Da Alhaji Lawan Zubairu da Alh Ibrahim Ahmad Katsina da Dr Kabir Mustapha. A cikin wadanda aka karrama dai akwai Alh. Lawal Aliyu Daura tsohon shugaban ma’aikata (Head Of Serbice) na jihar Katsina. Da  mai ba Gwamnan jihar Katsina shawara (Special Duties)  Alh. Tanimu Sada Mai taimakama Gwamna na musamman.

Justice Musa Danladi Abubakar shi ne ya mika wa Maigirma Gwamna da mataimakin sa lambar karramawar ta su. Sannan  Maigirma Gwamna ya mika wa ‘yan majalisun tarayya da na jiha. Mataimakin Gwamna ya mika wa Kwamishinoni da masu ba Gwamna shawara na musamman. Dan majalisar Tarayya mai Kankia, Kusada, Ingawa ya mika masu taimaka ma Gwamna na musamman.

Mai girma gwamnan jihar Katsina a nasa jawabin ya nuna mahimmancin aikin jarida da yadda ake son aikin ya kasance. ya kuma yi tsokaci kan kafofin yada labarai na social media. Gwamnan ya jajjadada kudirinsa na alheri ga al’ummar jahar tare da yi wa jahar fatan alheri.

Mai gayya mai aiki malam Danjuma Katsina ya nuna jin dadinsa da godiya da yabawa ga gwamnan jahar da maiatimakinsa kan yadda suke bayar da gudummawa a zauren sannan ya jinjinawa hakurinsu da juriyarsu. Sannan ya yabawa wadanda suka dau alhakin tsara taron karkashin jagorancin Alhaji Ibrahim Keegan. A cikin godiyarsa ya hada da wadanda suka bayar da kudi don tafiyar da taron.  Malam Danjuma ya godewa duk wanda yake cikin dandalin don kuwa da hadin kansu da bin dokar zauren musaman na kin amincewa da turo duk wani sako da ya shafi akidar Addini ko cin zarafi ga duk wani abokin adawa sannan ba a amince da turo labarin kanzon kurege da wannan zauren ya kai gaci har ya yi abin da aka yi a yau na ci gaba da zumunci da karrama junansu. An kammala taro lafiya bayan an ci an sha.

‘Yan jam’iyyar PDP da APC da ma sauran jam’iyyu na jahar sun halarci taron tare da faran-faran tamkar ba su taba yin wata adawa ba. Wannan yana nuna tasirin kafar sadarwa da a yau muke amfani da ita, in har al’umma za ta yi kyakkyawan amfani da ita kamar yadda ya dace shakka babu al’ummarmu za ta kai gaci a duk abin da ta sa a gaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: