Connect with us

RIGAR 'YANCI

Muhammad Ja’afaru Ya Lashe Kujerar Shugabancin NULGE A Jihar Nasarawa

Published

on

Mista Muhammad Ja’afaru ya yi nasarar lashe zaben shugabancin kananan hukumomi na kasa (NULGE) a zaben da aka gudanar a karamar hukumar Toto da ke Jihar Nasarawa.

An bayyana Ja’afaru a matsayin wanda ya lashe zaben ne bayan kammala zaben fidda gwani da aka gudanar a Nuwamba, 2019. Inda ya yi nasara da kuri’u 296 a kan abokin karawarsa wanda ya samu kuri’u 116.

Sabon shugaban, wanda babban jami’i ne a fannin fasaha kuma yana aiki a sashen filaye na karamar hukumar Toto, a yanzu haka zai jagoranci kungiyar a karamar hukumar Toto sashin NULGE.

LEADERSHIP A Yau  ta ruwaito cewa NULGE kungiya ce ta dukkan ma’aikatan kananan hukumomin kasar nan tare da rassa na Kananan Hukumomi wadda daukacin kananan hukumomi 774 na kasar nan ke karkashinta.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: