Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Zuciyata’

Published

on

Suna: Zuciyata

Tsara labari: Kabiru A. Yako

Kamfani: Hausa empire

Jarumai: Nuhu Abdullahi, Shu’aibu Lilisco, Hadizan Saima, Malam Inuwa, Asiya Mai Kyau, Kabiru Yako, Alhaji Garba, Ladi Mutu Ka-Raba da sauransu.

Shiryawa: Kabiru A. Yako

Bada umarni: Sulaiman bello easy

Sharhi: Hamza Gambo Umar

 

A farkon fim din an nuna Malam Inuwa ya dawo gidansa rike da wata jaka, yayin da matar sa nafisa ta tare shi da murna suka fara nuna wa junan su soyayya da irin kewar juna da sukayi. Daga nan kuma malam inuwa yaje yayi wanka ya sauya kaya ya fito don cin abinci, a lokacin ne matar sa ta ajiye masa wasu kayan lambu da ta zuba guba a ciki. A daidai lokacin da malam inuwa yayi yunkurin cin kayan lambun ne sai ‘yan fashi suka shigo cikin gidan suka rutsashi da bindiga akan suna so ya basu dalolin da ya shigo dasu a jaka, haka ogan ‘yan fashin ya tusa keyar malam inuwa suka nufi cikin daki, yayin da sauran yaran sa suka dauki kayan lambu da aka ajiye suka fara ci, bada jimawa ba kumfa ta fara fita daga bakin su nan suka fadi kasa a mace. A sannan ne kuma jami’an tsaro suka shigo gidan suka kama shugaban ‘yan fashi suka tafi dashi.

Malam Inuwa da matar sa suka je police station don jin ba’asin abinda ya kashe yan fashin da suka zo yi musu sata, a sannan ne Jami’in tsaro (Shu’aibu Lilisco) ya fada musu cewar an gano cewa guba ce a cikin kayan marmarin da suka ci kuma gubar ce ta kashe su, nan take Shu’aibu Lilisco yayiwa malam inuwa tambayoyi akan abinda ya sani daga nan kuma ya rutsa matar sa nafisa da tambaya gami da yi mata barazana don gano gaskiyar al’amari, nan take kuwa ta fada masa gaskiyar cewa ita ta saka gubar saboda tana so mijinta malam inuwa ya mutu sannan ta auri kanin sa Sadik (Nuhu Abdullahi) jin hakan ne yasa aka tsare ta sannan aka kira dan fashi don ya fadi inda sauran yan uwan sa suke, a sannan ne ya fadi cewa shi kadai ne kuma Sadik kanin malam inuwa ne ya tura su don su sato masa kudin yayan sa. Jin hakan ne yasa jami’an tsaro suka cigaba da tsare su.

A bangare daya kuma an nuna Salimat (Asiya mai kyau) a matsayin matar wan Sadik (nuhu abdullahi) Salimat ta kasance tana son kanin mijin ta sadik kuma ta kasa gaya masa hakan, yayin da shima yake son ta amma ya kasa gaya mata, a sannan ne ya fara ganin kanwarta Naja (Aisha yola) ganin ta ne yasa sadik ya kamu da sonta har ma ya tare ta a hanya ya fada mata abinda ke ransa, amma sai ta fada masa tana da saurayi, kuma ranta ya baci da ta dawo gida ta sanar da mahaifiyar ta (ladi mutukaraba) amma sai mahaifiyar ta ta rarrashe ta akan tunda ta fada masa gaskiya shikenan, kuma ta bukaci naja ta turo mata saurayin ta nura tana son ganin sa, bayan yazo ne ta sanar dashi tana son ya turo iyayen sa ayi maganar aure. Jin hakan yasa yayi murna gami da alkawarin zai turo iyayen sa.

Bayan wani lokaci sai sadik suka zauna suna hira da Salimat matar wansa har ta yanka kankana ta nuna saboda shi ta yanka amma sai sadik ya soma tambayar ta dalilin da yasa take bashi muhimmiyar kulawa, kafin ta bashi amsa ne kanwar Salimat wato naja ta shigo cikin gidan har ma ta sanar da sadik an kusa bikin ta don an saka rana. Jin hakan ne ya tashi hankalin sadik ya tafi yana tunani gami da cin alwashin sai ya aure ta takowane hali. A sannan ne malam inuwa ya kira sadik yake masa korafin matar sa nafisa bata dawo gida ba tun daga lokacin da jami’an tsaro suka bukaci yi mata wasu tambayoyi, ya nuna zai je ya duba abinda ke faruwa amma sai sadik ya nuna rashin goyon bayan sa akan hakan ya ce masa ya bari a kara jinkirtawa, amma malam inuwa bai amince da hakan ba ya tafi police station don jin ba’asin abinda ya hana matar sa nafisa dawowa gida. A police station ne Jami’in tsaro wanda ke rike da case din ya fada masa cewar sun gano itace ta zuba guba a cikin abincin da yan fashi sukaci suka mutu, yayin da kuma aka fito da sadik shima daga ma’ajiyar masu laifi akan cewa shi ya tura yan fashi gidan malam inuwa. Jin hakan ne yasa malam inuwa yayi tur da halin matar sa da kanin sa. Nan take Jami’in tsaron ya fadawa malam inuwa cewa zasu cigaba da rike nafisa da sadik har zuwa lokacin da za’a mika su ga kotu. Sadik da nafisa suka soma neman gafarar malam inuwa amma yaki kulasu har aka sake tafiya dasu ma’ajiyar masu laifi.

A bangare daya kuma an nuna sadik a zaune tare da mahaifiyar sa (hadizan saima) tana yi masa huduba akan kada yaso yayan sa malam inuwa domin dan kishiyar ta ne ita kadai ya dace yaso. Tun daga sannan sadik ya fara tunanin maganar ta har ya soma tunanin ta yadda zai mallake duniyar malam inuwa don su ci shida mahaifiyar sa, bayan yazo wajen mahaifiyar sa da zancen sai ta nuna ta amince da kudirin sa, daga nan aka nuna su a gaban malam inuwa yayi wa gwaggo (hadizan saima) alkawarin kujerar aikin hajji, tare da kyauta mai tsoka wadda zai yiwa sadik. Jin hakan ya sanya su murna amma bayan fitowar su daga gidan sai suka cigaba da tattaunawa akan shirin su na mallakar dukiyar malam inuwa.

 

Abubuwan Birgewa:

1- An samar da kayan aiki masu kyau, sauti ya fita radau, camera ma ba laifi.

2- maganganun jaruman wato (dialogue) sun kayatar.

 

Kurakurai:

1- An nuna lokacin da nafisa ta sakawa mijin ta guba a cikin kayan lambu, shin me ake son sake nuna wa mai kallo da har aka maimaita scene din har sau biyu?

2- Sunan fim din bai dace da labarin ba.

3- An nuna nafisa a matsayin matar malam inuwa, amma sai mai kallo ya cigaba da ganin Salimat a matsayin itace matar malam inuwa, shin matan sa biyu ne? Idan su biyu ne ya dace a bayyanawa mai kallo yadda zai fahimta, idan kuma labari ake bayar wa akan tsohuwar matar malam inuwa to ya dace a nuna alamun cewa an tafi labari sannan a nuna alamun an dawo daga labari ba wai a tafi da abin kara zube ba.

4- Mai kallo yaga sadik da yayan sa malam inuwa suna tattauna matsalar rashin dawowar nafisa daga police station, har malam inuwa ya nunawa sadik zai je yaga abinda ke faruwa. Amma bayan zuwan malam inuwa police station sai aka ga an fito da sadik a matsayin daya daga cikin masu laifin da aka kama, shin a yaushe har jami’an tsaro suka kamo sadik? Kuma tazarar dake tsananin hirar da sadik sukayi da yayan sa tayi karancin da za’a ce har yaje hannun jami’an tsaro.

5- lokacin da aka fito da sadik daga ma’ajiyar masu laifi, ya dace malam inuwa ya jira a fara yi masa bayanin laifin da sadik ya aikata, amma sai aka ga malam inuwa yana mamakin abinda sadik yayi masa na ha’inci, shin dama yasan cewa sadik ne ya turo ‘yan fashi gidan sa?

6- mai kallo yaga jami’an tsaro sun rike sadik da nafisa akan zasu turasu kotu a zartar musu da hukunci akan laifin da suka aikata, amma daga nan sai aka nuno sadik da mahaifiyar sa a zaune a cikin gida suna hira cikin raha kamar babu abinda ya faru, ya dace a nunawa me kallo dalilin da yasa ba’a ga an tura sadik kotu ko gidan yari ba, idan kuma har ya shiga ya fito ne ya dace a fadi tsahon lokacin da baki idan ma ba za’a rubutu ba.

7- An nuna nafisa tayi yunkurin kashe mijin ta malam inuwa har ma asirin ta ya tonu ta fada hannun hukuma, amma daga baya sai mai kallo yaga nafisa a zaune a gidan mijinta cikin kwanciyar hankali tare da mijinta. A rayuwa irin ta gaske babu mutumin da matar sa zata yi yunkurin kashe shi kuma idan ya gane har ya cigaba da zama da ita, wannan abu ne da baya yiwuwa.

8- Ba’a nuna karshen sadik da mahaifiyar sa ba wadanda ke da burin cin amanar malam inuwa.

9- Ladi mutukaraba da ‘yar ta naja tare da saurayin naja sam basu da amfani a cikin labarin, shin me ma a ke son nunawa a game da su?

 

Karkarewa:

Shin wane darasi fim din yake nunawa ne? Labarin sam bashi da jigo kuma bashi da doro, sannan kuma zaren labarin bai dire ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: