Connect with us

LABARAI

Gwamna Bello Ya Kirayi Masoya Da Makiyansa Bayan Rantsar Da Shi

Published

on

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a jiya Litinin ya yi kira ga jama’a, ciki kuwa har da abokansa da ma abokan hammayarsa na siyasa, da su jingine bambancin siyasa da akida waje guda tare da ganin sun hada hannu da gwamnatinsa, don kai jihar da al’ummarta tudun-mun-tsira.

Gwamnan, wanda ya yi kiran a wajen bikin rantsar da shi karo na biyu a matsayin gwamnan Jihar Kogi, wato ranar 27 ga Janairu, 2020 kenan, wanda alkalin alkalin alkalan jihar Kogi Mai Shari’a Nasiru Ajannah ya jagoranta a gidan gwamnati da ke birnin Lokoja, ya kuma sha alwashin cewa gwamnatinsa a mataki na gaba za ta janyo masu zuba jari na cikin gida da kuma kasashen duniya, don raya jihar.

Gwamna Bello, wanda tun da farko ya zayyano dimbin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a mulkinsa karo na farko, ya kara da cewa, ya dauki rantsuwa tsakaninsa da Allah da ya halicce shi cewa a matsayinsa na Gwamnan Jihar Kogi na hudu mai cikakken iko, zai gudanar da mulkin jihar bilhakki da gaskiya kuma ba tare da nuna bambancin yare, kabila, siyasa ko addini ba.

A don haka ya jaddada cewa, gwamnatinsa a zango na biyu za ta dora a kan dimbin nasarorin da ta samu. Ya ce,  samar da sha’anin kiwon lafiya, harkar noma, ilimi, harkar tsaro da samar da ayyukan yi da kuma abubuwan more rayuwa ga jama’ su na daga cikin manyan nasarorin da gwamnatinsa ta samu a baya.

Gwamna Bello ya kuma yi alkawarin cewa, a wannan karo gwamnatinsa za ta maida hankali a kan harkar noma, domin inganta cimaka da tsaro da ilimi da kiwon lafiya da kuma tara kudin shiga na cikin gida.

Har ila yau ya yi alkawarin cewa, ma’aikatan gwamnati a wannan karo na gwamnatinsa za su yi dariya har kunne, domin kuwa, a cewarsa, za su rika samun albashinsu a kan lokaci.

Daga bisani gwamnan ya godewa Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a bisa gagarumin goyon bayan da su ka ba shi a yayin mulkinsa karo na farko da kuma yayin da ya ke fafutukar neman tsaya wa takara a karo na biyu.

Har ila yau ya gode wa al’ummar Jihar Kogi a bisa fitowa kwansu da kwarkwatansu, don zaben sa a lokacin zaben gwamna da a ka gudanar a ranar 16 ga nuwamba, 2019.

Cikin manyan baki da su ka halarci biking rantsar da Gwamna Bello sun hada da Oshiomhole da da ministan sufuri Rotimi Ameachi da karamar ministan babban birnin tarayya, Hajiya Ramatu Aliyu Tijjani da gwamnonin jihohin Edo, Jigawa, Kebbi, Yobe, Nasarawa, Ondo da kuma Borno.

Sauran sun hada da mambobin majalisar dokoki ta kasa da na jihar da manya-manyan ’yan siyasa daga cikin da wajen jihar da sarakunan gargajiya da manyan ’yan kasuwa da kungiyoyin addini da magoya bayan jam’iyyar APC da kuma sauran jama’ a.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: