Connect with us

RAHOTANNI

Jami’in Hukumar Tsaro Ta Farin Hula Ya Harbe Dan Takarar Sanata

Published

on

A ranar Lahadi ne da yammaci wani dan takaran kujerar Sanata a yankin Okigwe, Honorabul Ndubuisi Emenike, ya rasa ransa ta hanayr harbin bindiga a wani abu mai kama da harbin a bisa kuskure da wani jami’ain tsaro na hukumar tsaro ta farar hula ya yi masa.

An ce jami’in tsaron da ya yi harbin yana tare da mamacin ne wanda ya yi takaran kujerar majalisar Dattawa a karkashin Jam’iyyar AA a babban zaben sekarar 2019 da ya gudana, inda yake aikin kare lafiyarsa.

Marigayi Dan Majalisar Dattawan yankin Sanata Benjamin Uwajumogu, shi ya lashe zaben, amma sai ya rasu a bayan watanni shida da kaddamar da shi.

Inda aka fara yakin neman zaben madadin na Benjamin Uwajumogu, inda aka bayar da rahotannin cewaNdubuisi, ne yake kan gaba a cikin sahun wadanda ake tsammanin za su lashe zaben.

Wakilinmu ya bamu rahoton cewa, hamshakin dan kasuwar mai bunkasar kiba ta jiki ya halarci wani taro ne a karamar hukumar Isiala Mbano, ta Jihar ta Imo, yana kuma kan gabar barin wajen taron ne sai jami’an tsaron na shi suka harbe shi har lahira.

Emenike, wanda aka fi kira da Ototonwa, an garzaya da shi Asibiti ne da ke can cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Owerri, inda Likitoci suka yi bakin kokarin ceto ransa daga Jini mai yawa da ya zuba daga gare shi.

Daruruwan mutane ne suka yi tururuwa zuwa Asibitin inda suke ta fatan samun lafiyar na mutumin da suka kwatanta da mai yawan alheri.

Jami’in tsaron da ya harbe shi din a bisa kuskure , wanda kuma ba a bayyana sunan sa ba, yana tare da mamacin ne na tsawon shekaru masu yawa tun ma kafin lokacin zaben.

Wata majiya ta ce, jami’in tsaron ya yi harbi ta fuskacin wajen da hamshakin dan kasuwan yake a bisa kuskure, kawai sai dai aka ga jinni yana bulbula a kasa.

A cewar majiyar, babu wanda zai ce maka ga ainihin inda aka harbe shi a jikin na shi a sakamakon jini mai yawan da ke zuba daga jikin na shi.

Mai Magana da yawun rundunar ‘Yan sandan Jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da yin harbin, amma ya ce lamari ne mai daure kai.

A watan Disamba da ya gabata ne, Sanata Benjamin Uwajimogu, mai wakiltar mazabar Imo ta Arewa, ya fadi kasa a sume, inda daga baya kuma ya mutu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: