Connect with us

TATTAUNAWA

Nasarar Ganduje Ce Zaman Lafiyar Jihar Kano – Shugaban Gawuna/Ganduje Foundation

Published

on

A wannan mako da muke ciki ne Babbar Kotun Koli ta Tarayya da ke Abuja, ta kori karar da Jam’iyyar PDP tare da Dan takararta, Abba Kabir Yusif, su ka shigar a gabanta na daukaka kara dangane da nasarar da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar ya samu, tun bayan zaben da aka gudanar a shekarar 2019 da ta gabata. Wannan dalili ne ya sa magoya bayan Jamiyar ta APC, ke nuna farin cikinsu sakamakon wannan nasara da suka samu. Wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA, ya samu ganawa da daya daga cikin masoya Gwamnan Jihar Kano tare da Mataimakinsa, wato Shugaban Gawuna/Ganduje Foundation, MALAM ISA BABA. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance:

Wannan Cibiya taku ta Gawuna/Ganduje ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin samun nasarar gwamna a Kotu, me za a fada wa mai karatu dangane da wannan nasara?

Ko shakka babu, wannan wani abu ne da wasu suke ganin kamar cewa lallai sai wannan gwamnatin ta je kasa, sannan duk abin da za a yi an riga an yi don ganin mai girma gwamna bai kai labara ba, amma duk abinda aka bar wa Allah, to fa ko shakka babu ya isar wa kowa.

Haka nan, gaskiya ne wannan Cibiya tamu tana da aikace-aikace iri daban-daban, wata rana idan mun samu isasshen lokaci za mu tattauna wannan, amma yanzu maganar siyasa kawai za mu yi. Kazalika, ya kamata mutane su san cewa duk abin Allah Ya rubuta zai faru, komakawa babu sai ya faru, babu wani tsimi babu dabara.

Gaskiya ne mun taka rawa iri daban-daban musamman a bangaren aiwatar da addu’o’i tare da shiga afafan yada labarai da sauran dukkanin wani kokari don tabbatar da ganin mun kai ga gaci. Sannan wannan Cibiya ta yi bakin kokarinta ba don komai ba, dalili kuwa akwai wasu abubuwa da wannan gwamnati ta faro kuma suna da muhimmanci a fadin Jihar Kano da kewaye.

 

Ko za ka fada mana wasu daga cikin wadannan ayyuka?

To ai wannan abu ne wanda ya fi rana haskawa a fadin Jihar Kano, domin duk inda ka bi za ka ga aiki ya mike gadan-dagan a cikin Birni da Kauyuka, ba don komai ba shi ne irin aikin da wannan gwamnati ta ke yi kowa ya san cewa gwamna ya kama hanyar kai Kano tudun-mun-tsira.

 

Mutanen PDP sun sa ran, kotu za ta kwace wannan zabe ta ba su, amma sai ga shi labari ya sha bamban, ba da wannan ake zargin gwamnatinku da karfa-karfa ba?

Da ma ai kai ma ka san wannan mafarki ne suke yi, domin kuwa kowa ya san an yi wannan shari’a a Kotun Korafe-korafen zabe ta Kano, an yi a ta daukaka kara, duk kuma an kore ta domin ba su da hujja. Saboda haka, in dai wannan shari’a ce duk inda za a je ba mu da shakku ko kadan, domin kuwa mun san mu ne da gaskiya tare kuma da nasara.

Sa’annan jagororinmu, kamar mai girma Gwamnan Jihar Kano da Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna, kowa ya san cewa mutune ne jajirtattu kuma masu kawaici, musamman shi mai girma gwamna an sha yi masa abubuwa marasa dadi amma sai ya kawar da kai, sannan sai Allah Ya hada shi da Mataimaki na kirki, babu wanda a yau zai ce ya samu korafi na wannan Mataimakin Gwamna, ko dai daga PDP ko kuma a APC, kowa nasa ne.

Har wa yau, ga Alhaji Murtala Sule Garo, idan ka dubi irin gwagwarmayar da ya yi ka san babu wata tafiya a APC, musamman a wannan gwamnati da za a bar shi a baya, domin mutum ne mai kokari da sanin ya kamata, kuma mutum ne mai nagarta da kuma amana. Idan Murtala ya ce zai yi maka wani abu, to kuwa ko shakka babu sai ya yi. Don haka, muna yi wa wadannan jagorori namu fatan Allah Ya kara musu kwarin gwiwa, su cigaba da gyara mana Jihar Kano. Saboda haka, shawarar da zan baiwa ‘yan adawarmu shi ne, su sani cewa Allah fa Ya rubuta hakan ce za ta kasance, fatanmu su zo mu hadu domin ciyar da Jihar Kano gaba tare da cire Matasa daga kangin da suke ciki.

 

Yaya kake ganin cigaban ayyuka a nan Jihar Kano, tunda yanzu an riga an kammala wannan shari’a?

Da a ce jiya ka biyo titin filin Sukuwa, wanda ya koma zuwa reskos, har bayan Sallar Isha’i aikin futulu ake yi, sannan kuma gwamnan ya yi alkawarin bayar da ayyuka a Kananan Hukumomi daban-daban na wannan jiha, domin su ma sauran mutanen Karkara su amfana da ayyuka, musamman na Rijiyoyin Birtsatse dakuma tituna. Sannan ga batun bayar da ilimi kyauta, tare da bayar da littattafai, ka ga kuwa idan ba mai kwazo ba wane ne zai dauki irin wannan nauyi?

 

Babban tsoron mutanen garinnan shi ne, idan wannan gwamnati ta cigaba da mulki batun haraji kadai ya ishe su, me za ka ce game da wannana?

Abinda nake so mutane fahimta a nan shi ne, batun harajin nan fa idan gwamnati ta karba kanmu yake dawowa, domin kuwa mu ake yi wa ayyuka da shi. Za ka ga mutum ya sayi mota ta Miliyan goma, amma kafin ta zo sai an biya mata duti da sauran abubuwan da ake bukata. Don haka, duk abinda aka karba a nan za a yi wa al’ummar wannan jiha aiki da shi.

 

Mene ne fatan wannan Cibiya taku?

Abinda zan ce shi ne, Allah Ya taimaki Gwamnanmu na Jihar Kano, Khadimul Islam, Ya kuma taimaki Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna da kuma Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo, domin kuwa dukkanin wannan nasara da muka samu su ne, silar jajircewarsu ce.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: