Connect with us

LABARAI

NIS Ta Sake Cafke Masu Safarar Bil’adama A Kan Iyaka Na Seme

Published

on

A cigaba da kokarin da take yi na dakile ayyukan bata-gari a kan iyakokin kasar nan, Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS), ta sake samun nasarar cafke wasu masu safarar bil’adama su uku da wadanda za a yi safarar su mutum uku zuwa kasar Ghana.
Jami’an hukumar da ke aiki a kan iyakar kasa ta Seme suka bankado mutanen tare da damke su nan take.
Kwanturolan NIS mai kula da ofishinta a kan iyaka na Seme, Olushola Ajisafe pcc+ da kansa ba sako ba ya jagoranci bincike mutanen, inda ya tabbatar da cewa lallai mutanen da aka cafken masu safarar bil’adama ne da wadanda suka fada kwomarsu. Ba wannan ne karon farko da Kwanturola Olushola yake rawar gani wajen damke masu safarar bil’adama ba, ya taba yin haka a lokacin da yake rangadin aiki a yankin Katsina, inda ya cafke masu laifukan safar bil’adama da dama.
Sanarwar da Shugaban NIS, Muhammad Babandede ya fitar ga manema labarai ta yi bayanin cewa, wadanda ake safarar tasu an yaudare su ne da cewa za a tafi da su a sama musu aiki mai tsoka, amma bayan an yi musu tambayoyi sai aka gano za a kai su waje ne da niyyar tsunduma su a karuwanci.
Shugaban hukumar ya ce, muguwar sana’ar safarar bil’adama tana kara kamari inda ake mata bad da kama da dodorido, amma kuma jami’ansa sun kasa-sun-tsare duk ta inda masu laifukan suka bullo za su cafke su, ta hanyar samun bayanan sirri a kan lokaci da kuma kyakkyawar alakar aiki da ke tsakanin jami’an hukumomin da ke aiki a kan iyakokin kasa na kan-tudu, da filayen jiragen sama.
Sanarwar wacce aka aika wa LEADERSHIP A YAU ta hannun jami’in yada labaran hukumar, DCI Sunday James ta bayyana cewa, Shugaban NIS Muhammad Babandede yana kira ga iyaye su kara sa ido sosai a kan ‘ya’yansu musamman wadanda suke matakin tashen balaga, domin galibi su aka fi yaudara da fadawa tarkon masu safarar bil’adama, wadanda za su iya kasancewa ‘yan’uwansu ne na kusa ko abokai, ko kuma bata-garin da suke haduwa da su a shafukan sadarwa na intanet.
Ya shawarci iyaye a koyaushe su rika neman shawarwari daga sahihan kwararru a kan tafiye-tafiyen ‘ya’yansu zuwa waje, domin rigakafin fadawa hannun masu safarar bil’adama.
Wakazalika, a wani labarin kuma, Jami’an Hukumar ta Shige da Fice (NIS) da ke sintiri a kan iyaka na Mazanya da ke hanyar Jibiya a Jihar Katsina sun yi nasarar cafke wani mai safarar bil’adama da wanda za a yi safararsa, inda bayan an yi musu tambayoyi aka tasa keyarsu zuwa babban ofishin Hukumar Yaki da Fataucin Bil’adama (NAPTIP) da ke Kano.
A tsakanin kwana uku dai, Hukumar NIS ta samu nasarar cafke akalla masu safarar bil’adama da wadanda za a yi safararsu su 23, ta filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas da wasu kan iyakokin kasa na kan-tudu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: